Gyaran Nono Ga Budurwa Da Matan Aure Kashi Na 3

Gyaran Nono Ga Budurwa Da Matan Aure Kashi Na 3

Nono (Breast) Yana daga cikin Ni'imar da Allah ya yiwa 'ya'ya mata domin su shayar da 'ya'yansu kuma Surarsu da kyawonsu ya kara bayyana.

.

Akwai tarin Abubuwa wayanda ke kwantar da Nonon 'ya'ya mata amma kafin mukai ga wannan bayanin ya kamata mu san ko (Breast din) kala nawa ne.

.

Bincike Ya nuna Breast din mata ya kasu kashi 8 daga cikin kashi 8 bincike ya nuna kashi 3 ne basa faduwa kashi biyar su suka fi saurin faduwa saboda sunfi kashi na farko girma.


Karanta>>> Maganin Gyaran Nono Mai Saukin Haɗawa


Idan Macce na kula da Breast dinta ko da yana cikin kashi 5 masu faduwa to wannan kular da take masa shi zai sanya ya ya cika cif-cif cif ba tare da an gane ya fadi ba.

.

MEKE KAWO ZUBEWAR NONO?

Akwai Abubuwa masu yawan Gaske dake kawo Zubewar Breast zan kawo wasu in bar wasu, Daga Ciki akwai;

.

1. Kwanciya Jicce.

2. Daurin Zane a Kirji.

3. Rashin cin abinci mai kyawo.

4. Rashin sanya Brr idan aka haihu.

5. Yawan Wasa dasu ba'a lokacin Jima'i ba. Dss.

.

WANE MATAKI ZA'A DAUKA DON GUDUN ZUBEWARSU?


Da Farko yana da kyau a lokacin da Macce ta haihu ta rika sanya Brr tana kwanciya da ita.

.

Na Biyu a guji Daura Zane a Kirji musamman Idan ba ana sanye da Brr ba.


Karanta>>> Yadda Za'a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi


Daga karshe a guji Kwanciya a Jicce.

.

YA ZA'A GYARA WAYANDA SUKA KWANTA?


Hanya ta Farko A nemi Man Hulba Cokali 2 Man Si'itir Cokali 2 Man Ridi Cokali 2 a rika shan Cokali 2 Sau 3 A yini. Sannan a Hada Man Hulbar dana Si'Itir a Rika shafawa a jikin Breast din ayi haka na tsawon Sati 4 In shaa Allahu za'a ga mamaki da Iznin Allah.


GYARA NONONKI DOMIN DAUKAR HANKALIN MAZA


TSAYUWARSU


ki kwaba hulba da ruwan dumi,wato garin hulba yadanyi kauri kar yayi ruwa sosai,saikin tabbatar kin gama abunda zakiyi,kinzo kwanciya,saiki shafa,ki kawo brezia damammiya kisaka,da safe saiki wanke da ruw an dumii,zakisha mamaki.


GIRMANSU


kisamu yis ,shima ki kwaba da ruwa mai dan dumi,saikin tabbatar kinyi kusan shiga wanka saiki shafa,akalla minti shabiyar ko goma saiki wanke.


Danna Bulun Rubutunan Domin Karanta Abubuwan Dake Haifar Da Tusar Gaba Da Hanyar Maganceta  


SU TSAYA SUYI LAUSHI


ki samu alkama ki wanketa,amma karki surfa saikin nikata,ki rinka sha da madara safe da dare


GYARASU SUYI KYAU


shine hanya mafi sauki,ya kasance kullum kina shafa man hulba akai,koda wanka kka fito,manda zaki shafa a jikinki daban ,nonon kuma hulban,sannan kina shan man yansun,cokali daya kullum.


Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Kashi Na Daya


LAUSHI DA DADIN KAMASU


kisamu garin hulba saiki saka cikin tafashashen,ruwa,saiki dauko tsumma ko towel,kina gasa nonon dashi,kina mammatsawa,inkika gama saiki,shafa musu man hulban.


BARI NA BAKU SHAWARA.


kisa shape din nonon da brzia da zakina sakawa, saboda kowanne da irinsa,kuma karki sa matsatstsen riga babu brezia,yana mata nono, da kuma zama da daurin kirgi duk, sunad matala, kidena kwanciya akan nono ki dena yawan tsalle da duk abinda zaisa su wahala.


MAGANIN CIWON NONO:-


A sami garin hulba sai a kwaba shi da tafashashshen ruwan zafi sai a shafe nonon tsawon yini daya sai a wanke washe gari sai a sake haka za'a dinga yi insha Allahu bada dadewa ba za'a samu sauki.


Karanta>>> Yadda Zaki Hada Kwalacca


MAGANIN AMOSANI:-


A sami man gelo da man zaitun da man kwakwa,sai a hade su waje daya a tafasa su da ruwan zafi sai a wanke kai dasu sosai a caccakuda kokon kai sosai da ruwan zafin insha Allahu kwana uku an rabu da shi.


MAGANIN CIWON MATA:-


A nemi man zaitun mai kyau sai a dinga shafe mara dashi, ko a sami zuma a hada da madara ta dinga sha.


MAGANIN CIWON KIRJI:-


A sami ruwan zafi ko shayi ba madara sai a matsa lemon tsami a zuba zuma aciki sai a dinga sha da sassafe kafin aci komai tsawon kwana bakwai kullum kofi daya insha Allahu za'a samu sauki.


Karanta>>> Tsumin Matan Aure Na Musamman Domin Inganta Zaman Aure


Post a Comment

0 Comments

Ads