Yadda Zaku Bude Profile Na JAMB/UTME 2023 Tundaga Yanzu

 


UTME 2023 : ZA KU IYA FARA BUÆŠE PROFILE DAGA YANZU.


 A shirye-shiryen ta, na tunkarar jarrabawar JAMB UTME ta shekarar 2023, hukumar JAMB ta bayyana cewar É—alibai za su iya Æ™irÆ™irar Profile Codes É—in su tun daga yanzu, su kuma adana shi, domin yin amfani da shi a lokacin da aka fara rijista.


 Hukumar JAMB ta bayyana hakan ne, ta cikin mujallarta ta mako-mako da ta saba fitarwa, a duk ranar Litinin, a babban birnin tarayya Abuja.


 Inda hukumar ta ce, hakan na daga cikin matakan da ta ke É—auka, dan tabbatar da gabatar da rijistar UTME ta shekarar 2023 lami-lau, ta hanyar kakkaÉ“e dukkannin wata É“araka, da matsaloli.


 • YADDA ZA KU ƘIRƘIRI PROFILE CODES :


 • Ku shiga wurin rubuta saÆ™on kar ta kwana na wayoyin ku (Messages), sai ku rubuta : NIN, ku kuma bada tazara, sannan ku rubuta lambobin katin É—an Æ™asar ku guda 11.


 Misali : NIN 12345678901.


 •Sannan sai ku aike da saÆ™on zuwa 55019, ko 66019.


 Daga nan, hukumar ta JAMB za ta aike mu ku da saÆ™on wasu lambobi guda 10, sai ku samu takarda ku rubuta su, ku kuma adana.


 KU SANI : Wannan tsarin ya shafi dukkannin É—aliban UTME da DE.


 Allah ya taimaka Ameen.

Post a Comment

0 Comments

Ads