"; Abban Sojoji Chapter 5 Complete Hausa Novel

Abban Sojoji Chapter 5 Complete Hausa Novel

```The father Of Soldiers```

        

Story 

     &  

       Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

 Fitowa ta yi tana leÆ™ensa, lalla6awa tayi ta Æ™araso gabansa kamar wata munafuka tace "barka da fitowa yaya Junaid," É—agowa yayi tare da kallonta ya ce "zan fita masallaci before na dawo pls a shirya min abinci bazan iya jurewa ba cos am starving," dariya ce ta kusa kubce mata hannu tasa a bakinta, harara ya jefa mata "dariyar uban me ka ke? 

  hannun ta cire daga bakinta tare da cewa "dama....ran nan ka ce min baka iya cin abinci saboda tare da brothers É—inka kke ce kun sa6a dole sai kun haÉ—u sannan kke ci atare shine...." tsayawa ta É—an yi tana kallonsa


sakin baki yayi yana kallon wannan É—an rainin hankalin É—an aikin nasu, rai abace ya ce "kai !! NI tsaran wasanka ne ? raini ya fara shiga tsakanin mu ko !" ya Æ™arasa maganar yana kallon ta, 

Hankalin ta ba Æ™aramin tashi tayi ba, bakin ta ya ja mata, 

  Saboda bacin rai muryarsa har rawa yake yi wurin kwalawa azmi kira,

  Nan fa ta aza kai a saman ka tana faÉ—in "wayyo Allah na Sorry sir," 

  duk a tunanin ta korarta zai sa ayi, jiki na rawa azmi ta fito baiwar Allah kana ganin ta kaga wadda bacci bai isheta ba, 


  Ƙaraso wa tayi tana faÉ—in "meya faru junaid kke kwalamin kira," 

Mayar da idonsa ya yi akanta ya ce "wannan mai aikin so nake nabasa punishment, cos he distains me , 

Ya Æ™arasa maganar tare da kallon sehrish ya ce " kasan yadda ake tsallen kwaÉ—i ko," cikin tsoro ta girgiza masa kai alamar bata sani ba, 

  Jinjina kansa yayi tare da cewa "amma kasan yadda ake up and down," 

Zuru tayi da ido don batasan me ake nufi da up and down ba, juya wa tayi ta kalli azmi, 


da ido azmi tayi mata alamar tace masa batasani ba,

Amma rashin fahimtar hakan yasa ta ce masa "eh na iya," 

cike da bada umarni ya ce "azmi inaso ki samun ido akansa, har nadawo daga masallaci nasame sa yana yi if not kowa zai gane kuransa," 

Yana gama faÉ—ar hakan yasa kai ya fice, 

Kallonta azmi tayi tana murmushi tace "oya start ae ke kika ce masa kin iya, ke kinsan menene up and down kuwa? mugun punishment ne mai wahalar gaske," 

murya na rawa tace" i don't know how to do it ," 

Dariya azmi tayi , tare da gyara tsayuwarta, ta some yin ƙasa da sama tana nuna mata yadda zata yi,

"Toh kin ga yadda zaki yi, maza ki fara kafin ya dawo sbd kowani lokaci zai iya faÉ—owa, ni zan koma ciki saboda haryanzu kaina ciwo ya ke min," 

tana gama faÉ—an haka ta shige ciki, zugudum sehrish tayi ganin ba kowa yasa ta lalla6a tasamu wuri saman 2 seater tazauna, daga taji motsi sai ta É—an firgita in taga bakowa sai ta natsu, 

zaman zuru tayi ga fargabar karya zo yasame ta zaune batayi abinda yace ba, bacci ne ya ziyarce da kuma dama kowa yasan bacci 6arawo ne, nan ta soma gyangyaÉ—i a hankaki yayi Wuuuf da ita, 


   Tsayawa yayi cike da mamaki yana kallon ikon Allah, mutumin da aka ba punishment ya shi baiyi ba, kuma yasamu wuri dirshen kamar É—an masu gidan ya kwanta, 

Jinjina kai junaid yayi wanda shigowarsa kenan, zuwa yayi inda tanÆ™amemiyar freezer É—insu take yasa hannu ya buÉ—e, robar ruwa ya dauko mai sanyin gaske har ya fara kankara, 

   Yana zuwa inda sehrish take, ta saki baki baiwar Allah sai sharar bacci take yi ga gashin bakin nan da take manna wa yamayar da ita wata yar cartoon guda, 

  BuÉ—e murfin robar yayin, kai tsare ya zazzage mata shi ajikinta, 

Wani irin firgit tayi ta farka lokaci guda ta tashi zaune jin yadda ruwa mai sanyin gaske yayi mata dirar mikiya,

  dogon numfashi taja tana sa hannayenta tana yarfo da ruwan dake zuba a fuskanta, idonta jawur ta É—ago ta kallesa,

  faÉ—a yasamo yi mata" saboda raini in saka ka aiki kazo kasami wuri ka zauna kana bacci ko kai ga riÆ™eƙƙen É—an bariki ko,"?

Saboda tsananin baƙin ciki fashe mashi tayi da kuka kamar jinjira, tama rasa me zata yi, me zatace masa

Ganin yadda tukur É—in ke shesshekar kuka yasa yaji kamar baiyi adalci ba, kasancewar junaid nada matukar tausayi wani sa'in, 

juyawa yayi ya mayar da robar ruwa, sannan ya dawo ya zauna kusa da ita, har lokacin kuka take kamar ranta ze fita,

Muryarsa ce ta ratsa sa" Am sorry" É—agowa tayi cikin mamaki tana kallansa bata ta6a tunanin zai iya bata hakuri ba,

Ci gaba da magana ya yi " ka gane am very simple man kaine ka cika sa ido,komai kaji sai kaja bakin ka kayi shiru karka sake mun haka !,"

Tsagaitawa tayi da kukan tace" kayi hkr bazan Æ™araba bazan Æ™ara ba insha Allah," 

yanayin yadda tayi maganar sai ya ji kamar muryar mace amma aduk lokacin da yaji hakan sai kawai yasa wa ransa cewa namiji ne saboda akwai waÉ—an da halittarsu ce hakan, 

"Its ok now i need something to it, go get it for me, am waiting ,"!

ya faɗi hakan cikin nuna buƙata, ta shi tayi ta nufi kitchen tana mai tunanin me zata sama masa ya ci, babban tashin hankalin ta azmi bata jin daɗi hakan na nufin cewa yau ita ce zata haɗa masu dinner kenan, gashi bata iya irin girkinsu ba na ƴan gayu,

da wannan tunanin ta shiga kitchen É—in, babu wani dafafen abinci sun cinye komai da safen nan, dole sai dai tayi preparing wani, cikin gaggawa cos he needs it immediately, 

cikin sauri ta za masa taliya saboda ita ce abu mai saurin dafuwa, kayan miya ta É—ebo ta gyara su ta markaÉ—esu , ta haÉ—a da kayan kamshi duka, ta jagwal gwala masa sai gashi ta fara Æ™amshi, murmushi tasaki "Allah sarki har miyau na ya gwada bari in zuba masa sai in rage saura nima inci," 

a cikin plate ta zuba masa ta haÉ—a masa da spork a ciki, lokacin da ta isa samun shi tayi yana daddana wayarsa, 

Cikin girmamawa tace "na kammala gashi," 

ajiye phone É—in yayi side É—insa sannan yasa hannu ya karba, a hankaki ya furta "shukran laka," 

maimakon ta tafi sai ta tsaya tana kallon yadda yake sargafo taliyar a cokali mai yatsun yana turawa bakinsa, da alama tayi masa daÉ—i, 

Sai wani ɗan murmushi take saki, ita dae a rayuwarta tana so tayi abu aci, hakan yana mata daɗi axuciyarta expecially da ya kasance junaid ne ke ci 😘

. Bata gajiya da kallonsa batasan meyasa ba amma tana da tabbacin cewa ba so bane na soyayya kawai burge ta yake yi, 

 ganin mai aikin tsaye akansa yasa shi tsagaita wa da tura abincin abakinsa ya ce "lafiya ka tsare ni da ido"?

da sauri ta girgiza kai tare da juyawa ta koma kitchen, zuba taliyar tayi itama ta samu wuri a É—aya daga cikin chairs É—in dake zagaye da dining table wanda ke a kitchen, ta soma ci farat É—aya zuciyarta ta tunano mata da wani abu nan take ta fashe da kuka mai cin rai , tura abincin kawai take yi amma ita kaÉ—ai tasan me take ji acikin ranta, 

Aduk lokacin da takai abu mai daÉ—i zata sa abakin ta, sai ta tuna cewa wani hali Æ´an uwanta suke ciki, me suka ci ? Shin suna samun abunda zasuwa cikinsu 

😥

   Babban tashin hankalin ta, shin ya aikin da akayi masu asibiti ke tafiya, husanna taji sauÆ™i ? shin ta rayu ko ta mutu saboda doctor yace ba tabbas ta rayu, 

   Cire hannunta tayi daga plate É—in abincin ta turasa gefe, tashiga matse kwalla, 

   Bata jinkirta ba har saida taji alamar shigowar mutun, cikin sauri ta shiga goge hawayenta don batasan wani ya gani balle ya tambayi dalilin zubarsu,

"Sehrish me kike yi a zaune, i think zanzo na same ki kin fara aikace aikacen fara girki," 

   tashi tsaye tayi cikin sanyayyiyar muryarta tace " ae mun afwa aunty azmi," 

Hmmm azmi ta tace , kafin ta wuce ciki domin fiddo kayan da zasu fara aiki da su,


Lafiyayyen abinci aka girka masu, fatan doya da wake, sakwara da miyar egusi taji kayan Æ™amshi ga naman ganda a ciki, farfesun iri biyu na kifi dana naman shanu, 

Saboda rashin lafiyar azmi yasa suka girka abinci kaÉ—an, saboda a kalla abincin dare suna yin kusan kala 6, 

Sehrish ce tayi aikin daka doyar tasha bakar wahala, azmi na kallonta sai dai tayi murmushi ganin yadda take faman zubda gumi, 

sai da ana kiran sallar magrib sannan suka idasa aikin, har time É—in ba wanda ya dawo daga cikinsu, junaid ne kawai wanda ke zaune yana a falo yana kallo a cikin laptop É—insa, 

bayan sun gama gyaggyara kitchen ɗin, ta wuce domin yin sallah ga kuma buƙatar watsa tuwa,

wani korean drama yake kallo (true beauty) series É—in yayi masa daÉ—i daga kwance saman doguwar kujerar ya ke kallo, ya kishingiÉ—a laptop É—in kuma na asaman cikinsa, 

Twins ne suka fara shigowa hannunsu riÆ™e dana juna, bai lura da su ba sai da yaji muryar Ayaan yana cewa "Lazy army we're back,' 

da murmushi a face É—insa ya miÆ™e zaune yana kallonsu ya ce" welcome back my brothers am glad to see you, nd i missed u,' 

Æ™arasawa sukayi atare suka manna masa kiss kowa agefen face É—insa, 

sannan Jahan ya ce "what are you watching my bro,' 

Junaid ya ce "its a korean series i really like it,' 

"Ohh thats good enjoy your self,' jahan ya faÉ—i hakan tare da sa kai suka wuce bedroom É—insu, 

Cike da zumuɗi suka shiga ciki saboda a ƙagare suke da su soma,

"gsky mai aikin nan tukur yana Æ™oÆ™ari kalli fa yadda ya gyara komai fes,' acewar jahan da yake Æ™oÆ™arin cire kayansa, 

Ayaan yace nima ina jinjina masa gaskiya kalli fa yadda muke hargitsa É—akin amma ya gyare sa tsaf,

 matsawa ayaan yayi kusa da jahan haÉ—e wa sukayi da junansu, a lokacin duk sun cire rigunansu da takalmansu, saura trouser É—in jikinsu shiga cikin juna sukayi sosai, haÉ—a ido su kayi cikin na juna tare da sakarwa kansu murmushi, zura harshensa ayaan yayi a cikin na jahan nan take suka soma nishi alamar kai ya fara É—aukan chargy, 

A hakan da suke a tsaye manne da juna, jahan yasa hannunsa agaban wandon ayaan ya zame masa belt É—in jikinsa, shima ayaan ya cire masa nasa kamar wasu mayu haka suka koma, ba sallah ba salati ba neman na É—an caka

"Tell me how did you feel it '? Jahan ya faÉ—a cikin wani irin salo a lokacin da yake bin jikin ayaan yana licking É—insa kamar yasamu Sweet

Zamewa Æ™asa yayi agaban ayaan yayi kneel down cikin wani irin salo, yasa hannu ya idasa zame masa trouser É—insa, 

Tuni ayaan ya gigita tajin abunda jahan ke masa nan fa suka fita hayyacinsu, 

Sai bayan sallar isha'e sannan sauran suka dawao kowa agajiye ya wuce bedroom É—insa,

A time É—in Junaid ya koma bakin swimming pool saman É—aya daga cikin chairs guda biyu dake kewaye da É—an table, 

wayarsa na ajiye a saman table É—in, bakomai ya ke tunani ba fa ce babban yayansu rafayet yayi kewarsa sosai, gashi ba kullum ake samun sa a waya ba sai in shi ya kira mutun, 

idonsa yakai yana kallon tsaftaccen ruwan dake malale a cikin faffaÉ—an pool É—in launin sa yayi blue sky gwanin burgewa ga wata irin sanyayyiyar iska wacce kai tsaye take ratsa sassan jikin mutun, natsuwa da kwanciyar hankali ne suka zo masa loka ci guda har ya soma tunanin ya É—auki wayarsa ya bibiyi numbar nan da aka turo masa message da ita É—azu,

É—aukar wayar yayi ya shiga laluban number cikin contact É—insa, dakyar ya gano ta , danna wa numbar kira yayi ta soma shiga ba'a É—aga ba.



Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!



*Katsina State*


Kwana 3 kenan da sallamo su daga asibiti, an basu magungu nan da zasu rinƙa sha na tsawon wasu kwanan ki, sun dawo gidan tsohuwa dama wurinta suke zaune a wani tsohon gida wanda ya jima da fita hayyacinsa saboda tsaban talauci , babban matsalar da suke fuskanta rashin abinci gashi doctor yace suna buƙatar su samu abinci mai gina jiki sosai ,duk sun rame bayin Allah ita kanta tsohuwar ta rasa yaya zatayi da su ita ke fafutukar yadda zata samu abunda zata ciyar dasu, dama ƙosai da kokko take yi da safe shine sana'arta toh sakamakon rashin lafiyar su komai ya ƙare mata jarinta ma ya karye komai ya ƙare musu ƙarƙaf,

A wani Æ™uÆ™uÆ™un É—aki suke kwana gidan É—aki biyu ne tabasu É—aya suke kwana ita kuma a É—ayan, 

Sam babu komai a É—akin kamar kango haka yake, yar jakar kayansu ce sai wata guiguyayyaiyar katifa wadda ko kyauta akan ban ita banaso sai dai na kwana a Æ™asa, 

Husanna na kwance a samanta idonta a rufe, ga busassun hayawe a fuskarta, kana ganin ta kasan taji jiki har ynx akwai wasu raunukan a jikinta,

Shigowa jahad tayi da lemar ruwa ajikinta alamar alwala tayo, cikin jakar kayansu ta É—auko wata tsohuwar hijabi ta sanya ta shimfiÉ—a wankakken É—ankwalinta a Æ™asa kasancewar basu da abun sallah, kabbara sallah tayi ta shiga karanta fatiha sbd sallar isha'e ce karatu a bayyane ake yinsa, 

takai raka'a ta biyu kenan taji muryar Husanna tana faÉ—in "sehrish sehrish ina so naje wurinta ina so naganta, nidai akaini wurinta bazan zauna a nan ba, 

Sallah take amma hankalinta atashe yake saboda sanin cewa husanna nada ciwon hauka in ta fara ba wanda ya isa ya dakatarta da ita, 

a firgice ta farka tana kiran sunanta tashi tayi a fujajen ta nufi hanyar fita É—akin cikin sauri jahad ta katse sallar saboda gidan da suke ciki bai da kofa buhu ne akayi kofar dashi in kuma husanna tafita hanya zata miÆ™a, 

ruÆ™o ta tayi da Æ™arfi ta janyo ta nan fa suka kacame da faÉ—a dama haka ake fama da ita, ga wani irin Æ™arfi dake gare ta saboda ba ita kaÉ—ai bace, cikin kuka jahad ke cewa "dan Allah kidaina ya kike so nayi da kaina ne! nima jiran kiranta nake yi kiyi hakuri kizauna,' 

muryarta har rawa take yi wurin faÉ—in "ni ita nake son gani, ki kaini wurinta ko ki ce mata tazo yanzun nan husanna nason ganin ta,' 

ganin dagaske husanna fita zatayi yasa ta Æ™ara Æ™anÆ™ame ta, aiko batayi wani aune ba taji tayi wurgi da ita sai gata baje a Æ™asa, nan take kuma goshin ta da hancinta suka fashe jini ya soma fito wa, 

a guje husanna ta fita jikinta daga ita sai É—aurin gaba kanta ba É—ankwali, sai tarin uban gashin dake gare ta mai yawan gaske ga tsari irin mai buzu-buzun nan mai kanan naÉ—ar indomie , ya zubo mata har side by side É—in fuskanta, 

tana gab da zata fita tsohuwa tashigo cikin gidan hannunta É—auke da kwano ta samo musu abincin da zasu ci, 

Aikuwa karaf suka ci karo da husanna tuni kwanon hannun tsohuwa yayi sama ya faÉ—o kasa wainar dake ciki ta zube cikin Æ™asa, 

saboda tsabagen takaici yasa tsohuwa tafashe da kuka cikin kuka tace" kinsan wahalar nada sha kafin nasamo muku wannan wainar, sai da akayimun wulaÆ™anci da girma na da shekaruna kafin akaban ita bashi, amma kalki yadda kika zubar da ita kasa....' kasa idasa maganar tayi cikin kunar rai ,  

tsayawa husanna tayi jikinta yayi mugun sanyi saboda ita ba a cikin hayyacinta tayi ba, hasalima ta manta meya faru ita dai kawai taga tsohuwa na kuka agabanta, nan ta shiga tambayarta meya faru meyasa take kuka, 

fitowa jahad tayi itama tana shesshekar kukan, juyawa husanna tayi tana kallonta cikin mamaki tace "wai meya faru meyasa kuke kuka pls tell me ?

Ƙarasa wa jahad tayi gaban tsohuwa cikin lallami tace" kiyi haƙuri dan Allah, kin sha wahala sosai akanmu duk da baki da wata alaƙa damu, akanmu ba irin wulaƙancin da ba'ayi miki ba amma ki kara jure insha Allah wahalarki baxata tafi abanza ba, Allah zai kawo mana mafita,

tana gama faÉ—an hakan takarasa inda kwanon wainar ya Æ™ife cikin Æ™asa, zukunnawa tayi ta kwaso ta saman guda uku ce Æ™asar bata shiga sosai ba, kwaso wa tayi ta zuba cikin kwanon ta miÆ™e da nufin taje ta wanko ta, 

cikin sauri tsohuwa ta ruÆ™o hannunta tare da cewa" kin manta lalurar da ta same ki, idan har kikaci wannan wainar ciwonki zai iya dawo wa, ki aje kawai zanje na sake samo wani bashi tunda bazan barku da yunwa ba,' 

gaba É—aya jikinsu yayi sanyi tsananin tausayin kansu ne ya kamasu, juya wa tsohuwa tayi zata fita jahad tace "dan Allah ki aramana wayarki mu kira sehrish dama saboda ita ne haukan Husanna ya tashi," 

Tsohuwa tasa hannu a ha6ar zaninta ta zaro yar nokia É—inta wadda ake kira da rakani toilet ta miÆ™a wa jahad tare da cewa "na manta in faÉ—a miki naga kiran wannan numbar da sehrish ke kira da ita ban É—auka ba ynx sai ku kira ta,' 

Wani irin farin ciki ne ya baibaye su, jin cewa sehrish takira su kara su , karbar wayar jahad Tayi tare da riÆ™e hannun husanna tace mu shiga ciki mukira ta, sam husanna takasa rufe bakinta burinta taji muryar Æ´ar uwarta akwai abubuwa dayawa da take so ta faÉ—a mata waÉ—anda ke damunta, 

Abuja city........

message É—in Fawan ne ya shigo wayrsa karantawa yayi "kai kana ina gayanan zamu fara É—a'amin kashigo ciki," 

Murmushi ya saki tare da miÆ™ewa ya shiga ciki samunsu yayi kowa ya hallara a dining table É—in, zama yayi shima binsu yayi da kallo kowa ya shirya tsaf, twins nasanye da kimono robe ajikinsu, irfan da jabir nasanye da jallabiya fara, kanal yusif ya kimtsa cikin pyjamas É—insa haka khaleed da jabeer ma, 

Cikin girmamawa ya shiga gaishe su amsa wa suka shiga yi, kafin kowa ya soma jiran isowar tukur mai aiki don yayi serving É—insu, 

  É—agowa khaleed yayi ya kalli su twins ya ce "Oh shegentaka iri iri ynx ku wannan har abun sawa ce Æ™irji a waje ,guiwowi a waje ,' yaÆ™arasa maganar yana jiran amsa 

" kai kuma ubansa ido naga cewa duk maza muke kaima in kaso u can wear ur shots nobody will disturbs u,' jabeer ne yayi maganar yana harararsa,

  shima khaleed É—in harararsa yayi ya ce "am i talking to u stupid mind your own business if not u will see the rest,' 

  dariya irfan yayi "kai kun cika faÉ—a kamar kaji," 

  fawan yace " kaji fa kace ? Just like a women ina laifin kace kamar zakaru," 

 dariya sukayi su duka sai lokacin kanal yusif ya tsoma baki "twins kunburge ni da baku sa baki ba, halin girma kenan,' 

  ta6e baki fawan yayi "a ina girman ya ke a tanan, kalle su fa kamar mata Ayaan ya tara uban gashin kai gayanan ya sauka har kafaÉ—arsa kamar wata mace,' 

tsoki Jahan yaja jin an ta6a masa rabin ransa don haka ya ce"tubarkallah masha Allah aniyarka tabi ka, kuma yaje ya tara sumar kansa ne ko naka' 

  cike da jin dariya fawan yace "nasa ne, amma kasani duk ranar da Babban yaya ya dawo wlh duk sai kun aske kawunanku,' 

   ambatan sunansa yasa duk sauran jin bugun zuciya, murmushi junaid yayi tare da cewa " u ave to get ready cos he informs me about his coming very soon,' 

  Shiru su kayi gaba É—ayansu kamar malam yaci shirwa ayaan ya ce "Are you serious about what are u saying !" cikin tashin hankali yayi maganar, 

Junaid ya ce "of course" 

 Kallon juna suka yi shi da Jahan cikin rashin natsuwa, 

  Adai dai nan sehrish ta Æ™araso dama bacci ne ya kwashe ta, bayan tagama sallar isha'e 

     sai faman Æ´an kame kame take, tayi tunanin zasuyi mata faÉ—a amma saita same su tsit kowa shiru tunda aka ambaci sunan babban yaya jikinsu yayi la'asar, 

gaishe su ta fara yi sannan ta jinkirta tana jira taji me zasu je, 

Yusif ne ya ce "ka zubamin farfesun naman nan asa mun romo sosai sai a haÉ—amin da slide bread a sama,' ta amsa da to tafara zuba masa ta miÆ™a masa, 

twins suka bada umarnin asa musu sakwara da miyar egusi wadda taji naman ganda 6aro 6aro, haka ta zuzzuba musu, sai Æ™amshi ke faman tashi haka tabi sauran ta sassa musu wasu fatan doya da wake , shidai junaid farfesun kifi yace asamasa har fawan na jansa faÉ—a "karasa abunci sai farfesun kifi salon kaje kaita Æ™arni,' 

murguÉ—a masa baki yayi tare da cewa"ina ruwanka,' 

bai Æ™ara cewa wani abu ba, binsu tayi É—aya bayan É—aya tana ajiye musu cup mai É—auke da abunsha, 

Sun natsu suna turawa cikinsu abinci wayar junaid ta shiga ringing , tissue ya yago ya goge hannunsa sannan ya dauko wayar daga cikin aljihunsa, ganin numbar É—azu yasa shi É—aga wa saboda dama jiran kiran yake yi, 

"Amma kasan dai an hanamu picking calls while we're eating food so u break the rule now,'? Fawan ne yayi maganar yana kallonsa, harararsa junaid yayi baice komai ba saboda ya sanya waya a kunnansa, 

ji yayi kiran ya datse hakan na nufin flashing ne aka yo masa, bin kiran yayi tana fara ringing aka É—aga, sa wayar yayi a handsfree yadda kowa zaiji me ake cewa, sallama yayi sannan ya saurara yana jiran mai wayar yayi maganar 

"Aslm yar uwa jahad ce muna ta jiran kiran ki tun kwanaki baki kiramu ba,meyasa ?' 

Saboda tsabagen ruÉ—in jin muryar jahad yasa sehrish sakin cup É—in dake hannunta wanda ta zubawa Ayaan coffe cikinsa, nan take ruwan coffee É—in ya 6arar masa a hannunsa har Æ™irjinsa yayi tsalle ya É—iga, tsananin zafi yasa shi fidda wani sound me Æ™arfi, 

Hakan yasa junaid katse wayar da yake yi saboda ganin halin da Ayaan ya shiga , gaba É—ayansu sun raxa na musamman jahan wanda rai , a6ace ya yunkura ya mike ya sharara mata mari har sau uku at the same time, 

Cikin kunar rai yake cewa "wannan wane irin rashin hankali ne twin bro É—in nawa kake so ka halakar, mutumin da ko sauro bai ta6a cizon fatarsa ba sai kai zaka illatar dashi.


Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!


Ba ƙaramin zafin marin nan sehrish taji ba, don kuwa har hancinta sai da ya fashe cikin kuka take basu hakuri " kuyi hakuri bada sani na hakan ya faru ba bazan ƙara ba,

tsawa fawan ya daka mata "hakuri fa ? A wannan babban laifin da ka aikata zamuyi maka hakuri dole ka É—anÉ—ani kuÉ—arka kasancewa agidan Abban sojoji kake aiki,!" 

duk sai junaid yaji jikinsa yayi sanyi ganin yadda mai aikin yake ta zubar da hawaye amma ba yadda zaiyi kuskurensa ne!

cikin tsananin 6acin rai Jahan ya ruko hannun Ayaan suka shiga ciki saboda ya shafa masa magani don wurin har yayi jawur ya tattare, 

dukar da kai sehrish tayi tana jiran sauran hukuncin da zai biyo baya, 

Fawan ne yaso ma magana " ka fara tsallen kwaÉ—i daga nan har zuwa saman stair ka zakayo ta É—ayan stair É—in ka kewaye falon gaba É—aya haka zaga dinga yi har mu kammala cin dinner É—in mu, bayan nan akwai wankin motoci kusan goma da sukayi Æ™ura sun jima a ajiye, a wanke su tsaf duk a cikin daran nan nakeson hakan, sannan ba shikenan ba gobe akwai wani horon,' 

ba Æ™aramin tashin hankali ta shiga ba jin irin wannan muguntar da fawan ya tsara mata, ta razana sosai saboda girman wurin babban tashin hankalin shine tsallen kwaÉ—i a saman matattakalar bene har biyu ya abun zai kasance? 

muryarsa ce ta katse ta "Oya start frm now, we're watching you banda tsayawa if u do so you will see the trouble,' 

Zukunnawa tayi ta fara tsallen kwaɗin ta miki hanya ta tafi , idonta cike taf da hawaye damuwa iri iri, tasha wahala fiye da tunanin mutun tun tana yi cikin daɗin rai har kafafunta suka soma rirriƙewa ga wani irin raɗaɗi da suke yi mata, numfashin ta ne ya soma fita agalabaice amma haka ta jure ta daure taci gaba da yi , lokaci guda ta hada jini da majina a fuskarta hancin ta yasoma bleeding dama tana yi in taji wuya, babban tashin hankalin ma nan take period ta balle mata jini ya soma zuba ta ƙasan ta Subhanallahi ,

tana jin É—iÉ—É—igar wani abu ta cikin pant É—inta yana gangarowa amma batasan menene ba, Allah yaso wandon jikinta baÆ™i ne bazaiyi saurin bayyana ba, shi dama jinin al'ada sometime bakar wahala na kawo sa a time É—in da bakayi tsammani ba, 

Sam junaid ya gaza samun natsuwa yarasa dalilin dayasa yake jin tausayin tukur É—in nan mai aikinsu, ganin bazai iya jure ganin wannan zaluncin na fawan ba yasa shi tashi cikin sauri yabar table É—in duk da bai koshi da abincin ba ya miÆ™i hanyar zuwa É—akinsa yana hawa saman stair É—in suka ci karo da ita alokacin take saukowa , dakyar take numfashi kamar kwaÉ—o haka ta koma , bin kafafunsa tayi da kallo a hankali ta É—ago da idonta wadanda suka kaÉ—a su kayi jawur ta kallesa shima a lokacin  idonsa nakanta da take zuÆ™unne hannunta ruÆ™e da kunnuwanta, 

Ido cikin Ido suke kallon juna tazama gwanin ban tausayi baiwar Allah, shi kuma amatsayin namiji yake kallonta tsananin tausayi ne ya kamasa a hankali ya furta "Am sorry" cikin wannan sanyayyiyar muryar tasa, yana faÉ—in hakan yabi ta gefenta ya haye sama, 


Sai da kowa yabar dining table ɗin amma fawan mugu yana nan zaune yana jira mai aikin nasu tukur yagama punishment ɗin daya basa, sannan suje ya nuna masa motocin da zai wawwaken duk acikin daren nan kusan ƙarfe 9,_

JUNAID

tun da ya shiga room É—insa ya gaza samun natsuwa tunaninsa yaron nan mai aikinsu tukur bai kamata abarsa yayi wankin motoci cikin daren nan ba saboda shima mutun ne kamar kowa, in akai masa hakan ba'ayi masa adalci ba! 

Tunano wa yayi da maganar babban yayansu (talaka da mai kuÉ—i duk É—aya suke a wurin Allah babu wani banbanci don haka kada ku kuskura don Allah yabaku wani matsayi aduniya kuce zaku wulaÆ™anta wanda ke Æ™asa da ku domin bakusan Wace rana zai yi muku ba, kuma Allah zai iya kar6e wannan matsayin da kuke taÆ™ama dashi yaba shi wannan wanda kuka Æ™asÆ™antar aranar ya zakuyi ? kowa zai iya kuskure a rayuwarsa amma aduk lokacin da wani yayi maka badai dai ba kazamzo mai hakuri da yafiya domin Allah ma yana gafarta mana in mukayi ba dai dai ba sai mu Æ´an adam zamu gaza yin haka bazamuyi koyi da manzon Allah (SAW) ba ?  

tuna wannan maganar yasa shi fita cikin sauri ya , cikin gaggawa yake saukowa down stair a lokacin har sehrish ta sume a Æ™asan last step É—in benen, shi kasan fawan baisan hakan ya faru ba saboda wayarsa yake ta faman daddanawa , 

Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yadda me aikin nasu yake sume a kwance ba numfashi ,

tsallake sa yayi ya wuce inda fawan ke saune sai faman murmushi yake yana daddana waya ,

Kamar daga sama yaji an fizge wayar daga hannunsa, cikin sauri ya É—ago yana kallonsa yace "Junaid wannan wane irin abune zaka sa hannu ka fisge waya daga hannuna kamar wani tsaranka,' 

harara junaid ya wurga masa tare da cewa "bansani ba! saboda tsabagen mugunta irin taka kasa wancen mai aikin wahala wadda tasa shi sume wa amma sam baka damu ba ," 

tsoki fawan yasaki tare da sa hannu ya ƙarbe wayarsa ya wuce tagabansa yana faɗin "Matsalarsa ce,"

Binsa da kallo yayi har ya shige bedroom É—insa, 

Ba yadda junaid ya iya dole ya koma inda tukur ke sume yasa hannu ya É—aukesa, sam baima san ina ne inda É—akin kwannansa yake  ba , 

Amma yasan cewa bazai wuce kwanar da É—akin azmi take ba, kama hanyar yayi , ko nauyi baya ji haka ya dauke ta kamar yar baby ,

cikin sa'a ya samu É—akin,da kafarsa ya turo kopar É—akin ya shiga da ita , a saman bed ya kwantar da ita 

Ransa ne ya basa ya dauko ruwa a freezer yazo ya yayyafa masa , yana sa hannu zai buɗe kofar idonsa yakai a jini dake hannunsa, har sai da gabansa ya faɗi rass ! ya soma tunanin jinin menene wannan !!! 😳


Bin jinin da kallo yayi tunani yayi kodai kansa ne ya bugu ayayin da ya sume a gefen stair, 

Don haka cikin sauri ya koma yahau saman gadon inda ya kwantar da shi, a hankali yasa hannunsa yana tattare hular dake kanta a ƙoƙarinsa na ya cire hular yaga ta inda jini ke zuba,

Can kuma ya fasa saboda ganin yadda fuskar tukur É—in ta dame da jini da majina, handkchief ya zaro daga front pocket É—in rigarsa, ya shiga goge mata fuskarta, 

Kwatsam gashin bakin da take manna wa a fuskarta ya ya goce saboda ya jigata gashi dama gam gare sa ruwa ya taba sa sosai , 

Hankalin junaid ba Æ™aramin tashi yayi ba ganin ya cirewa tukur gashin bakinsa duk sai yaji ba daÉ—i yakai hannu domin ya gyara sai yaga ya ballo gaba É—aya, da ya Æ™ura ido yana kallon Æ™asan hancin sai ya gane cewa dama babu gashin bakin fixing É—insa akayi, 

Saboda babu hudojin gashi a wurin sai kansa ya É—aure ya gaza gane menene dalilin liÆ™a gashin baki, 

tabe bakinsa yayi alamar i don't care, ci gaba da gogewa yayi ana haka sai ya ga gashin girar ta da aka liÆ™a masa shima ya zame gefe guda, tashin hankali a fili ya ce meke faruwa ne wai 

Hannunsa ya sa ya ciro gashin girar duka guda biyun nan take asalin jagirarta mai kyau ga tsari ta bayyana, 

Natsuwa yayi ya Æ™urawa face É—inta ido sai yaga fuskar ta koma ta mace sak ! Kansa ya gama É—aure wa sanya gashin girar dana bakin yayi cikin handkchief É—insa ya naÉ—e su ciki ya ajiye gefen bedside drawer É—inta, 

Ya jima yana kallon wannan kyakkyawar fuskar har lokacin bai kawo wa ransa cewa maca ba ce ba sai da yasa hannu ya tumbuÆ™e hular dake kanta, nan take gashin kanta ya tarwatse ya warwaro har saman shoulder É—inta mai kyau ga laushin gaske, 

Nan fa junaid yayi zuru yana ganin wannan ikon Allah ( wonders shall neva ends)

ganin ta soma motsi zata farka, yasa shi yin wuff ya dira daga saman bed É—in ya boye abayan curtins É—in dakin, 

buɗe idonta tayi waɗanda suka cika tab da kwalla, sunyi jawur sun ƙanƙance, wani irin raɗaɗi taji a marar ta, gashi sam ba ƙwarin jiki atattare da ita, wata irin kasala ce ta dabaibaye ta a galabaice ta miƙe tana zubar da hawaye, yunƙurawa tayi tare ɗan matsawa gefe nan taga jini malale a saman bedsheets ɗinta ya baci sosai ,

Wani irin mugun bugu xuciyarta tayi mata saboda ita sam batasan jinin menene ba, saboda bata ta6a yinsa ba wannan ne karo na farko a wannan shekarun nata 17years,

lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka ganin jini 6aro 6aro na fitowa daga jikinta, cikin kuka take faÉ—in "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un shikenan na mutu wayyo Allah wannan wane irin ciwo ne naji haka, nasan mutuwa zanyi 

tashi tayi a firgice tasa hannu ta cire zanin gadon ta nannaÉ—e sa ta ajiye sa anan, 

gaba É—aya ta fita hayyacinta ta zabure kamar wata mahaukaciya  tama rasa me zatayi , cikin toilet tashi ge tana kukan baÆ™in ciki , 

A jiyar zuciya junaid yasaki, har yanzu ya gaza gasgata abunda idonsa ke ganin masa, shin wanene wannan tukur mai aikin mu ko kowa ? kamar mace nake gani fa, oh my God mafarki nake ko gaske, kodai idanuna ne ke nuba min hakan taya tukur mai aikinmu zai kasance mace !! Ya jefa kansa wannan tambayar 

Hannu yasa tare da murxa eyes É—insa don yayi comfirming abinda ke faruwa cewa gaskiya ne its not a dream, 

yana nan tsaye la6e a bayan labulen yana jiran fitowarta, saboda ya gane wa kansa zahiran abunda ke faruwa ,

Sehrish kuwa tamkar ranta zai fita, saboda tsoran jinin da ta gani ga kuma Æ™yanÆ™yami daya kamata, 

cire wandon jikinta tayi sannan ta cire rigar ma, hannu tasa ta balle abunda take matse ƙirjinta dashi tayi wurgi dashi,

ta firgita da ganin yadda jinin yake gangarowa a tsakankanin cinyoyinta  kai kace fanfo aka buÉ—e,

Cikin tsananin tsoro ta ƙarasa gaban fanfo tashiga dambe da jinin nan ita ala dole sai ta dakatar dashi daga fitowa 😟

Tana wanke wa yana sake kwaranyo wa kamar ana ingiza shi,

ganin yaƙi tsayawa yasa ta dakata, ta zuƙunna a wurin tana kuka tayi mai isarta, sannan ta yanke shawarar ta koma cikin bedroom ɗin ta samu wani abu ta cusa, sam ta manta cewa pant ɗinta ɗaya ne kuma ya bace shima, koda me zata sa ?

A haukace ta fito cikin sauri junaid ya rufe idonsa tare da jan labulen ya rufe face É—insa, bai jin daÉ—in tsayawa ba saboda yaga abunda yake haramin agare sa sam babu kaya ajikinta, 

Jikinsa ne yasoma kerma nan take yadinga jin zuciyarshi na tashi ynx ya tabbatarwa kansa cewa tukur mai aikinsu zankaÉ—eÉ—iyar budurwa ce ba namiji ba, shigar maza kawai take yi saboda wani dalili nata, 

buÉ—e wardrobe É—in tayi saboda rashin natsuwa duk ta watso da kayan dake ci tashi ga laluben É—an kyallen da zata sa, wani mayafi ta É—auko sai da ta riÆ™e sa gam a hannunta sannan ta tuna cewa bata da pant É—in da zatasa, 

zuÆ™unne wa Æ™asa tayi ta shiga rera wani sabon kukan, gwanin ban tausayi jin har yanzu wannan blood É—in yana mata flooding a under É—inta yasa ta koma cikin toilet tana kuka, 

Shiga tayi taja kofar ta rufe ...

Ganin ta shige yasa junaid saurin fita daga É—akin, tafiya yake amma tunanin yadda zai taimaka mata yake yi saboda ya gane cewa akwai abubuwan da take buÆ™ata, amma tayaya? bayaso ta gane cewa ya ganta a matsayin mace, baisan wani hali zata shiga ba, 

Maganar abbansu ya tuna a inda ya ke cewa

 _aduk lokacin da kuka ga wani na buÆ™atar taimako, to kutaimaka masa indai kuna da halin yin hakan, a sanadiyar hakan kuma Allah zai agaza muku a lokacin da kuka shiga wani hali na rayuwa," 

Cikin sauri ya hanzarta nufar bedroom É—insa , key É—in motarsa ya dauko tare da kuÉ—i , sannan cikin gaggawa ya kama hanya ya fita daga main palour É—in ,

Babu kowa tsit kake ji amma ko'ina akwai haske kamar rana, saboda an Æ™awata gidan gaba É—aya da wasu irin electric bulbs, 

Moto park É—insu ya nufa buÉ—e inda tarin motocinsu ke nan, motarsa yayi ya shiga nan take yayi mata key yaja ta, 

Sam junaid ya manta cewa security guards É—in gidan soldiers ne kuma bana wasa ba, kuma ba'a basu iznin subar wani ya fita a wannan lokacin ba kosu fawan dake satar hanya su fita night club su suka san ta boyayyiyar hanyar da suke fita, 

Santal ya miÆ™i titin da zai sada ka da babban gate É—in gidan, yana isa wasu gabza gabzan sojoji guda 4 suka tunkare sa kamar zakuna, 

a dolensa ya dakata da tuƙin ya tsaida motar, jikinsa sai rawa yake yi ba don komai ba sai don uzirin dake gare sa, zuge glass ɗin motar yayi yana kallonsu a yatsine, .

"Where are you going in this darkness night,"? É—aya daga cikinsu ya tambaya yana kallonsa, banza yayi baice musu komai ba don yasan koya ce É—in ba barinsa zasu yi ya fita, rigima ce zata tashi Æ™arshe suce zasu sanar da Abbansu a tada hargitsin duniya, 

jin yayi shiru yasa É—aya daga cikinsu daka masa tsawa tare da cewa "maza ja mota ka koma gida Æ™aramin yaro dakai sai taurin kai,' 

ÆŠaya daga cikinsu ne ya kwatsa ma wanda yayi masa tsawa magana" stop shouting at him ! he's a young lallashinsa ya kamata kayi ya koma " 

xukunno wa yayi cikin lallami ya ce masa "pls go back ba'a bamu izni mubar wanin ku ya fita ba daga gida a wannan time É—in,' 

girgiza kai junaid yayi tare da cewa "am sorry to say i won't go back just allow me to go, duk rigimar da za'ayi sai dai ayi amma ba inda zani i will stay here till u give me the permission to go,' 

Ya Æ™arasa maganar tare da jingina kansa jikin kujerar motar yana kallonsu fuska adaure" 


Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!



Post a Comment

0 Comments

Ads