"; Abban Sojoji Chapter 22 Book 2 Complete

Abban Sojoji Chapter 22 Book 2 Complete

 

```The father Of Soldiers```

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)



Sam jahad ta gaza yin kwakkwaran motsi saboda ta riga ta gane muryar wacece.......

Idasa shigowa tayi da wannan takun nata, jikinta na sanye da sleeping dress red colour masu zanen flowers ajikinsu, abunka ga fara ta fito 6au acikinsu, kanta ko mayafi babu ba kowa bace wannan face AUNTY BABBA,

Lokacin da ta isa inda jahad take, hannu tasa ta fisge takardar da take rubutawa, ta É—ago da ita tana karanta wa, zaro ido tayi hankali tashe tace "Keeeeee! Don ubanki ni zaki tonawa asiri!? Wato Omar kike rubutawa wasiÆ™a don ki faÉ—a mashi abunda muke yi maku ! Wlh kin shiga uku, bazan Æ™yale ki ba sai kin yabawa aya zaÆ™inta!!!! 


a masifance take magana Æ™arshe tayi  Wurgi  da takardar Æ™asa sannan azafafe da wannan hannun nata Æ™irar samudawa ta damÆ™o mayafin dake lullu6e akan Jahad nan take ya sul6e Æ™asa hakan ya bata damar damÆ™ar gashin kanta, wani irin zafi ne ya ziyarci jahad saboda ruÆ™on da aunty babba tayiwa gashin kanta,

    Janyo gashin tayi ta É—ago jahad dashi, jikinta sai kerma yakeyi duk ta rurruÆ™e hannun aunty babba dake ruÆ™e da gashin kanta tana faÉ—in "Aunty dan Allah kiyi haÆ™uri bazan Æ™ara ba....' bata Æ™arasa ba aunty babba takai mata naushi a bakinta, nan take jini ya soma zuba daga bakinta le6enta suka faffashe, saboda tsananin azaba da raÉ—aÉ—i yasa jahad fashewa da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali,

   Wurgi da ita aunty babba tayi jahad ta tafi jiki a mace ta zube Æ™asa, tattakawa aunty babbba tayi izuwa inda take don bata gama dukan nata ba,

   Tashi zaune jahad tayi tana jan jikinta da baya da baya tana faÉ—in "dan Allah kiyi haÆ™uri bazan Æ™ara ba.....nasan nayi kuskure....

   "Ke Æ™aramar Æ´ar iska ce ! bakisan koni wacece ba ! Har ni zakiyi wa iya shege acikin gidana ! Ni zaki tonawa asiri Wurin Omar? idan na so yanzu saina sa wuÆ™a na yanka ki, shashasha...

ta Æ™arasa maganar tare da sake damÆ™o gashin jahad tashiga yi mata azaba dashi, ta ja shi da Æ™arfi tamkar zata tsige shi daga kanta, tuni idon jahad yayi jawur wasu irin jijiyoyi suka firfito mata a goshin ta, don rashin imani aunty babba sai ta naÉ—e gashin a wuyan jahad ta shaÆ™eta dashi gadan gadan zata kashe ta, murya ashaÆ™e jahad ke fidda sounds tana faÉ—in "Ahh...ah..ann...bazan..Æ™a..ra..ba' sam aunty babba bata da niyar Æ™yale ta sai ma Æ™ara shaÆ™eta da take yi 

   Kamar daga sama Hosana ta faÉ—o É—akin saboda tajiyo ihun jahad da farko sai tayi tsammanin kunnanta ne Suke mata gixau,amma rashin kwanciyar hankali da jin bugawar zuciya yasa hosana gaza samun natsuwa ta fito don tazo taga wani hali jahad ke ciki ta rubuta wasiÆ™ar,

  Shine ta taras da wannan tashin hankali, ihu tasaki a haukace ta watsa da gudu inda aunty babba ta shaÆ™e jahad ajikin wardrobe, 

  "Kada ki kuskura ki Æ™araso in ba haka ba zan haÉ—a dake kema," aunty babba ce tayi ma hosana wannan maganar batare da ta janye hannunta daga wuyan jahad ba, cikin kuka hosana ke faÉ—in "ki sake ta...! Ki kyale ta....kada ki kashe mun Æ´ar uwata.....' amma sam aunty babba taÆ™iya,

   Ganin jahad ta soma kakarin sheÆ™awa barzahu yasa hosana fita hayyacin ta, 

aikuwa ta daddage da iya Æ™arfinta na Æ™arshe tasamu damtsen hannun aunty babba ta Gartsa mata lafiyayyen Cizo da hakoranta 30 cufffff 

   A firgice aunty babba ta saki jahad tana yarfa hannun ta sai ga jini na É—igowa, cikin hanxari tasa É—ayan hannunta ta zame hannun rigar jikinta don taga inda hosana ta cije ta, wurin yayi jawur ga sahun haÆ™oran hosana nan rerass a farar fatar hannunta dama gashi dumurmur na Æ´an hutu,

   Cike da jin raÉ—aÉ—i tace "Innalallahi !ni kika ciza har kika fasa mun fatar jiki na !! Ya salammmm !! Kin mutu wlh !! Kin shiga uku !! tayi maganar idonta jawur saboda taji raÉ—aÉ—in cizon hosana wurin har wani Zogin azaba yake yi mata,

   Ja da baya hosana tashiga yi a tsorace ganin aunty babba na tunkaro ta Kamar Damusa, gashi jahad tunda aunty babba ta sake ta, ta sulale ta sume a Æ™asa balle itama ta taimaki hosana,

   Hanyar fita ta nufa da gudu zata fice, cikin rashin sa'a aunty babba tasanya Æ™afarta ta taÉ—iyo Æ™afar hosana, aikuwa ba Æ™aramin buguwa hosana tayi ba, gaba É—aya ta kife Æ™asan tiles É—in É—akin, fuskarta ta dake sa, nan take hancinta ya fashe jini ya soma kwaranyowa, haka goshinta ma ya fashe da La66anta duk sun farfashe ihun azaba kawai hosana ke saki tana faÉ—in "wayyo Allah na ....! Nashiga uku...na mutu na lalace !! 

   Aunty babba tace "baki mutu ba, don ubanki, yanzu ne zaki mutun.....tayi maganar tare da kai hannunta kan Gashin hosana wanda ya barbaje Æ™asa, kwakkwarar damÆ™a takai masa, ta ruÆ™o shi dakyau ta janyo hosana dashi har sai da hosana ta miÆ™e tsaye tana ihu kamar ranta zai fita, daddagewa aunty babba tayi da iya Æ™arfinta na Æ™arshe ta buga kan Hosana jikin bangon É—akin wayyo Allah zoka ga yarda jini ya wanke bangon,

Razanan nan Ihu hosana tasaki na azaba tamkar maƙoshinta zai ballo waje nan take ta sulale ƙasa a mace.......


Ihun da hosana tayi na ƙarshe wanda ya karaɗe ko'ina harya sa Hafsat dake kwance ɗakinta saman gadonta farkawa a firgice, ta diro daga saman gadonta jiki na rawa ta fito ta tunkari inda sautin ke fita cikin hanxari ta faɗo ɗakin,

  gabanta ne yayi wani irin bugu ganin Momynta a tsaye tana huci kamar wata zakanya, ga kuma twins É—in da Omar ya kawo a baje Æ™asa jina jina musamman hosana an zubda jini

   Hankali tashe hafsat tace "Mommy me nake gani haka !! Me kika yi masu ne !! Kashe su Ki kayi da hannun ki !!!

   tsawa aunty babba ta daka mata tare da cewa "Eh kashe su nayi,akwai magana ne ! babu ruwanki dani ki koma É—akinki zai fi miki," 

  Cikin rauni hafsat tace "mommy duk rashin imani na bazan iya aikata abunda kika aikata ma yaran nan ba, ashe baki da Imani ko misÆ™ala zarratin ! Kisan kai da hannun ki........' 

  Bata idasa maganar ba saboda jin saukar wani irin zazzafan mari a kuncinta, tashin hankali da ba'a sama shi rana, 

    Saboda zafin marin da aunty babba tayi ma hafsat yasata dafe kumatun ta ido jawur take faÉ—in "Mommy yau ni kika mara da hannun ki"? 

    "Naje na mara ! duk kece sular da kika 6atamin raina harna aikata abunda na aikata yanzu!!"

    shiru hafsat tayi yayin da idonta ke fitar da wasu irin siraran hawaye masu zafin gaske,

  Jikin aunty babba ne yayi mugun sanyi ganin hawayen dake fita a idon hafsat Æ´arta tilo,

    Cikin tashin hankali tace "ba da son raina nayi hakan ba ! Hafsat ke kika 6atamun rai da 6acin ranki na kwanta, cikin daren nan na fito saboda zuciyata batamun daÉ—i kawai naga yarinyar nan jahad ta nufo É—akin nan shine na biyota in ga mai zatayi ashe wasiÆ™a zata rubutama Omar akan abunda muke aikata musu, da nufin inyazo su bashi.......yanzu yaya zanyi hafsat....na kashe su ba'a hayyacina ba...In Omar yazo bansan me zan faÉ—a masa ba......" tayi maganar tana yarfa hannunta idonta cike tab da hawaye cikin tashin hankali, 

   Murya na rawa hafsat tace "Mommy kin ja mana masifa da bala'e duka, ni banji xafin marin da kikayi mun ba, domin wannan kaÉ—anne akan Marin da zamu kar6a ni dake a wurin Yaya Omar wlh bazai Æ™yale mu ba !! Yadda kika kashe su ke ma haka zaisa ayi maki hukuncin kisa babu ruwana ......

   Cikin shesshekar kuka aunty babba tace "Hafsat yanzu don na kashe waÉ—an nan tsintattun marasa galihu nima sai Omar yasa akashe ni? 

   A tsiwace hafsat tace "Eh.!! dama menene alaÆ™arki da Shi da zai tausaya miki? Kwarama Ni zan tsira ke kuwa Yayansa kawai kike aure !! Wlh mommy kin shiga uku gaki can an garÆ™ame ki a cell Æ™arshe a yanke maki hukuncin É—aurin rai da rai har sau biyu saboda rai biyu kika kashe.......

    Hannu aunty babba ta aza akanta tana faÉ—in "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un nashiga Uku Ni LAILA naja ma kaina mutuwa a lokacin da ban shirya ba, 

      Jiki a mace aunty babba ta zuÆ™unna inda hosana take kwance a mace tana faÉ—in "kee!!!kee!!! tashi !! Maza ki tashi don ubanki ! Wlh baxa ku jamin bala'i ba, hafsat É—auko mun robar ruwa a fridge dan Allah in yayyafa musu ko sun tashi

    tayi maganar tana kallon hafsat, fuce wa hafsat tayi da sauri sai gata ta dawo hannun ta É—auke da bottle water ta miÆ™a mata, kar6a Aunty babba tayi jiki na rawa ta cizge murfin tashiga yayyafa ma hosana ruwan ajikinta, 

   Gabansu ne ya faÉ—i atare ganin hosana ko motsi batayi duk sanyin da ruwan yayi hakan na nufin ta mutu kenann !!!!!!

  tuni fuskar aunty babba tayi jawur kamar wadda aka nannausa saboda tashin hankali 

A ruÉ—e tace "Hafsat mun shiga uku !! Mun lalace !! Wlh ta mutu wayyo Allah na ni laila......

    Hafsat dake tsaye hankali atashe itama aruÉ—e tace "wlh Mommy laifinki ne, kece saurin fushin tsiya ga zafin zuciya gashi nan kin kashe su, To ni wlh babu ruwana aciki, dama ban da wata alaÆ™a dake haihuwata kawai kikayi.......

   É—agowa aunty babba tayi ta kalle ta ido jawur cikin disashewar murya tace "Hafsat ni kike ce ma baki da wata alaÆ™a dani, saboda Æ™addara da tsautsayi sun rutsa dani.....'

   Cikin kuka hafsat tace "Ae gaskiya na faÉ—a mommy ! ina bacci na kin katse mun shi da wannan tashin hankalin, Allah mommy ba abunda zai hana Omar yasa a garkame ki a cell , har na hango ki cikin kayan gidan yari Allah bazasu yi maki kyau ba yadda kike haka É—in nan........' tayi maganar tana nuna aunty babba dake zuÆ™unne agaban hosana kamar buhun masara,

  "Yanzu ya zamuyi ? Hafsat kar6i robar ruwan ki yayyafa ma É—ayar muga in ita zata tashi, wataÆ™il ita In tafarka sai in samu sassauci awurin yanke mun hukuncin......

   Cikin sauri hafsat ta kar6i robar ruwan dake hannun aunty babba ta Æ™arasa inda jahad take tashiga yayyafa mata shi a fuskarta, Wani irin dogon numfashi jahad taja kafin tace "La'ila ha illallah Muhammad rasulillah....

    Ganin jahad tafarka yasa aunty babba tashi tsaye ta tunkare ta tana faÉ—in " Alhamdulillah saura É—ayar yaya zamuyi hafsat ? Kodai kawai mu binne gawarta a cikin garden É—in gidan nan ne? 

   Wani irin kallo hafsat tayi mata tare da cewa "ashe mommy hankalin É—iyar roba ke gare ki? mu binne gawa acikin gidan nan ? Idan fatalwarta ta tashi fitowa ke zata fara ziyarta Allah,

   Hannu aunty babba ta aza akai tana faÉ—in "Ya salam duk ni naja ma kaina"

   daker jahad ta buÉ—e idonta wanda suka kumbura sukayi jawur, ga le6anta sunyi sutum sutum inda aunty babba takai mata naushi,

   Idonta bai sauka akan kowa ba sai kan hosana dake baje Æ™asa jini duk ya wanke fuskarta......

  Da Æ™arfi ta furta "Hosanaaaa !!!!!!!!!,' tamkar bakinta zai tsage yunÆ™urawa tayi ta tashi a tsananin razane ta Æ™arasa inda hosana ke kwance ta zube saman guiwowinta tana faÉ—in "hosana ki tashi ! mai ya faru dake ne? Wa yayi maki haka !! Innalallahi'wa'inna ilaihirraji'una .....ta Æ™arasa maganar tare da kifa kanta jikin hosanar tajima bata É—ago ba sai daga baya ta É—ago da kan nata tana faÉ—in "Dan Allah ku kaita asibiti kada ta mutu !! Kada narasa Æ´ar uwata," 

  Kallon juna su kayi sai yanzu suka mayi tunanin zuwa asibiti don sam basuyi tunanin hakan ba, 

   Jiki na rawa hafsat tace "mommy ki É—auko ta, bari naje room É—ina naÉ—auko mukullin mota mu tafi," 

   Aunty babba tace "Toh,ki tahomun da mayafi dan Allah"

  fucewa hafsat tayi tana faÉ—in "kiyi sauri mommy," 

   Cikin hanzari aunty babba ta Æ™arasa jiki na rawa, ta cuccu6i hosana ta aza aka faÉ—arta ta fuce da ita daga É—akin, itama jahad ta bisu abaya

    Fitowa hafsat tayi itama a lokacin har aunty babba ta buÉ—e back seat na motar ta kwantar da Hosana aciki itama jahad tashiga ciki sannan ta rufe,

   Su kuma suka shiga front seat hafsat na a mazaunin driver ita kuma tana a gefenta,

   Da gudu hafsat ta tada motar taja ta a tsiyace suka nufi hanyar fita daga gate É—in gidan

   Nan take sojojin dake gadin gidan suka tunkaro su don jin ba'asi

  Aikuwa a masifance aunty babbba ta É—aga murya tana cewa "Nice nan zan fita kar in ga wani shege ya tare mun Æ™opa Wlh in bi takansa....' 

  Jin muryarta yasa su kayi baya baya suka bata hanya ta wuce.......... da gudu suka miÆ™i titi sai asibiti, kuma duk da haka sai da sojojin nan suka biyo su abaya saboda aikinsu ne basu tsaro musamman acikin daren nan,


Suna isa asibitin gudu gudu sauri sauri Aunty babba ta É—auki hosana suka shiga ciki,da hanzari reception nurses suka karbe ta aka shiga da ita ciki, anci sa'a an samu likitan dake a bakin aiki, cikin gaggawa suka shiga duba hosana,

  Su kuwa su aunty babba da hafsat suna atsaye sai faman zagaye suke kowa cike da zullumin abunda zai biyo baya in yarinyar ta mutu, jahad kuwa tana abakin É—akin da aka kwantar da hosana ta kwantar da kanta jikin door É—in idonta na tsiyayar da hawaye masu É—umi,😭

Gaba É—ayansu babu wanda ya samu bacci adaren nan saboda da tashin hankali, 

   (Na zubda hawaye saboda halin da su Hosana da jahad suke ciki Ya Allah ka kawo masu É—auki) 😭

______________________________________


Ana cikin kiran sallar asuba Sehrish tafarka a hargitse tana faman dafe saitin zuciyarta dake yi mata wani irin raÉ—aÉ—i, sai faman ambaton sunan Allah take yi, tabbas ranta na bata cewa wani mummunan abu ya faru dasu Jahad, cikin hanzari ta sauko daga saman gadon tana faman zagaye É—akim kafin daga bisani ta shiga cikin toilet ta É—auro alwala, 

  Fitowa tayi ta nufi wardrobe É—inta, hijab ta É—auko da darduma ta shimfiÉ—a, ta shiga jera sallah, bayan ta kammala ta zauna tare da É—aga hannayenta sama tana addu'o'i akan su hosana da jahad da sauran al'ummar musulmai, ta jima tana addu'ar kafin ta koma saman gadon nata ta kwanta tana fuskantar sama abubuwa iri iri na zuwa mata aranta daga bisani bacci ya kwashe ta, bata sake farkawa ba sai Æ™arfe 10 na safe,

Firgit ta farka har time É—in shiga kitchen ya wuce,

  Zumbur ta miÆ™e shaf shaf ta shirya cikin shigarta ta maza da ta saba, saboda zullumi bazai barta ta fita a matsayin mace ba, a hankali ta tura Æ™opa ta fuce izuwa kitchen, 

  Bin ta da kallo azmee tayi wadda ke gyara kitchen don harta kammala breakfast É—in already tun É—azu,

  Da mamaki tace"Sehrish ya akai naganki kuma da shigar maza? 

   Shiga ciki tayi tana cewa "Aunty azmee ni tsoro nake ji Allah," 

   "Wani irin tsoro kuma,ba wani tsoro abunda nake so dake bayan mun kammala jera abinci, sai ki koma É—aki ki cire wannan gashin bakin ki sauko da gashin kanki zan kira ki, sai ki fito a matsayin mace"  

Shiru tayi tana kallon yatsun hannun ta kafin tace "shikenan Allah yasa komai ya tafi adai dai,


Murmushi azmee tasaki tare da jinjina kai tace"Insha Allah yanzu bari na fara jera miki warmers É—in kina kaiwa dining,"


  Ta amsa mata da "toh", tana jin É—ar axuciyarta 


  Cikin Æ™anÆ™anin lokaci suka kammala jerawa, Ayaan da Jahan ne suka fara fitowa sanye cikin kakinsu gwanin kyau, Suka samu wuri suka zauna kusa da Juna, azmee ta soma saving É—insu, time É—in sehrish ta shige bedroom É—inta don ta kimtsa kamar yadda su kayi da azmee zata fito a matsayin mace,

 Bayansu sai kanal yusif ya fito shima sanye da Jallabiya launin ruwan toka, wuri yasamu yazauna yana gaishe da aunty azmee, da fara'a take amsa musu, cikin girmamawa su twins suka gaishe shi shima ya amsa musu daga bisa ni kowa ya mayar da hankali kan breakfast É—insa,

  Sehrish na cikin É—aki cike da zullumin yarda za'ae ta fito a matsayin mace, tana a jikin Æ™opar É—akinta tana ruÆ™e da handle É—in kopar cike da fargaba,

  Gyaran murya azmee tayi ta É—an É—aga murya tare da kwaÉ—awa sehrish kira da sunanta tace "Sehrish ki fito mana," 

Jin sunan da azmee ta ambata yasa su kallonta da mamaki, sake maimaitawa tayi "Sehrish ki fito nace," 

  Kallon juna Ayaan da jahan su kayi sannan suka kalle ta atare suka haÉ—a baki wurin cewa "Wanene Sehrish kuma? Kanal yusif shima cike da mamaki yake kallon azmee jin sai faman kwala kira take yi, zuba ido su kayi don suga wanene wannan sehrish É—in da Azmee ke faman kira, shin baÆ™o su kayi ne a gidan nasu ko kuwa?

  buÉ—e Æ™opa sehrish tayi gabanta na faÉ—uwa ta tunkaro hanyar dining area É—in, jikinta na kerma a tsorace take tafiya, 

  gaba É—ayansu suka É—ago suna kallon ta tun kafin ta idasa bayyana a area É—in da suke, bin Æ™afafunta su kayi da kallo waÉ—anda ke sanye da Æ´an silifas É—inta na gado, sai faman kerma yatsun Æ™afarta suke yi, 

  Time É—in da sehrish ta idasa fitowa a raxane jahan ya miÆ™e tsaye, ayaan kuwa baisan lokacin da ya saki cokalin dake hannunsa ba ya faÉ—a cikin plate É—in dake agabansa, kanal yusif kuwa kallon abun yake kamar a mafarki,

  Bin ta suke da kallo cikin mamaki,  kamar a mafarki suke kallon lamarin, Æ™arasowa tayi ido a zazzare jiki na kerma, riga da wandon nan ne ajikinta , ta cire gashin bakinta, ta kuma zuba da doguwar sumar kanta har gab da waist É—inta, ta fito asalin macen ta Tsaleliyar budurwa Æ´ar matashiyya,

   A rude jahan yace "Azmee who's she ?  daga ina ta faÉ—o cikin gidan nan? Da iznin wa!?

  Ayaan kuwa cewa yayi "Ku kuke ganin mu bamu muke ganin ku ba ! Wannan Hurool ainin fa? daga aljanna ta gudo? 

   Kanal yusif sam yagaza magana bayani kawai yake jira daga wurin azmee, ita kanta azmee ta É—an razana da reaction É—in da suka bayar, Sehrish kuwa a gefen azmee ta tsaya tana faman zare ido,

  "Azmeee Explain !!!!' jahan ya faÉ—i azafafe harda dakar table É—in gabansa da tafin hannunsa,

   Murya na rawa azmee tace " Kuyi haÆ™uri dan Allah...Am wannan da kuke gani ba kowa bane face Tukur mai aikin ku, nasan zakuyi mamakin hakan......

  Dakatawa tayi ganin yarda Ayaan da kanal yusif suka miÆ™e atare, cike da ruÉ—u Kanal yusif yace "What ! Wai wane tukur É—in ake magana ! Ba dai wannan yaron mai aikin namu ba, kina nufin dama mace ce ba namiji ba ....? Ya tambaya hankali atashe ,

   Daga sehrish har azmee sun tsorata, 

   Hannu jahan yasa yasake bugun table É—in abincinsu yace "Impossible bazai ta6a yiyuwa ba ! muddin kuwa hakan ta kasance dole yarinyar nan ta fuskanci hukunci mai tsanani kuma tabar gidan nan ayau É—in nan,

  Fashewa da kuka sehrish tayi saboda tsorata da maganar Jahan gashi idonsa na akanta ya zare su, 

  "Dan Allah ku kwantar da hankalin ku, laifi ne nasan ta aikata amma kuyi mata afwa, sam bata da niyar cutar da kowa.....' dakatar da ita Ayaan yayi da cewa "Ba wannan zancen ! Saboda Æ™arfin hali irin na Yarinyar nan, tayo shigar maxa ta saje acikin mu tana mana aiki, babu sirrin mu da bata sani ba, babu irin firar da bama yi agabanta, har yawo muke yi da towel a Æ™ugunmu, muyi yawo da gajerun wanduna duk idonta na akai, kaf ta haddace ashe kallon mu kawai take yi," 

bil'haƙki ayaan yake kora bani, gaba ɗayansu ba komai suke ji mawa ba face yadda sehrish ta saje A cikinsu matsayin namiji na tsawon lokaci tana masu aiki, duk a tsammaninsu namiji ne ashe maca ce, tagama sanin sirrinsu saboda babu irin firar da basa yi agaban ta, sannan babu irin shigar da basa yi suna yawo duk a idonta,

  Hannu Jahan yasa yana Æ™oÆ™arin zare belt É—in wandonsa da nufin ya jibgi sehrish saboda yafi kowa fusata, gashi dama su Mace bata agabansu balle suga kyanta ko wani abu haka don su tausaya mata,

 A tsorace sehrish ta Æ™anÆ™ame kanta ta 6oye abayan aunty azmee tana faÉ—in "Nashiga uku ! Dan Allah aunty azmee ki basu haÆ™uri, kada su buge ni...zan tafi nabar musu gidan,

   ture kujerar gabansa yayi gadan gadan ya tunkari sehrish zai jibge ta, 

  Kamar daga sama suka ji Muryar Abban su yace "Kada ka kuskura ka ta6a ta!'

  Atare suka É—ago suna kallonsa kowannan su na huci, 

  RuÆ™e yake da hannun junaid cikin nasa, yana sanye da jallabiya junaid kuma na sanye cikin riga fara da wando baki, ya tsorata da ganin halin da sehrish ke ciki gashi kuma yayi mamakin ganin ta ta bayyana kanta a matsayin mace, ga kuma jahan tsaye ruÆ™e da belt wato zai jibge ta, 

  Idasa isowa sukayi inda suke tunkan abbansu yace wani abu Ayaan yace "Daddy dama wannan yaron tukur mai aikin gidan mu mace ne ba namiji baa !!

  murmushi Abbansu yasaki yana kallon su yadda duk suka zabura, 

Mayar da idonsa yayi kan Yarinyar dake 6oye abayan azmee yace "Ke zonan," 

   "Sehrish ki fito Abbansu na kira,"

Azmee ce ke tunasar da ita, fitowa sehrish tayi jiki na kerma ta Æ™arasa inda Abbansu yake tsayawa tayi at front of him murya na rawa take faÉ—in "dan Allah kuyi haÆ™uri ku yafe mun, nasan nayi laifi wlh ni banzo da niyar na cutar da kowa ba.....' 

   tsawa Jahan ya daka mata da cewa "Rufe ma mutane baki kona zo nan na nakaÉ—a miki shegen duka," 

    Abbansu yace "Ya isa haka Jahan, bana so kowa yasake magana," shiru su kayi gaba É—ayansu suna sauraron mai abban nasu zai ce,


Shin ina haroon duk wannan abun dake faruwa yana a tsaye fitowarsa kenan, gaba É—aya ransa ya gama jagulewa mamakinsa yarda akai yarinyar ta bayyana kanta A matsayin mace bayan bai idasa cimma burinsa ba, na tsoratar da ita,  Amma ganin yadda su Jahan suka fusata yasa shi jin daÉ—i aransa burinsa karsu amince su tada 6alli sai anyi mata horo sannan a koreta shi kuma zaiyi amfani da wannan damar wurin Æ™untata mata,


 tsayawa yayi da murmushin mugunta a fuskarsa don yaga ya Æ™arshen bada'Æ™alar zata kaya, 

Daga shi sai gajeran wando fari ajikinsa tsaye ruƙe da ƙugu, ɗayan hannunsa na ruƙe da Brush da alama ma daga toilet ya fito,


 burinsa yaji mai Abban nasu zai ce,

 gyaran murya Abbansu yayi sannan ya soma cewa "Na riga da nasan komai game da yarinyar! Domin junaid ya jima da sanarmun komai agame da ita, duk abunda junaid ya nuna yana so aduniyar nan koma menene shi zan amince dashi, Junaid ya nuna cewar yana son Zaman yarinyar nan agidan nan, don Haka Na AMINCE masa,!"

  Cikin mamaki suke kallon abban nasu, Haroon kuwa tuni yayi wata irin raxana har Brush É—in dake hannunsa ya faÉ—i Æ™asa sbd jin abunda Abbansu yace, 

  Murmushi kawai junaid ke saki, kallonta Abban su yayi tare da cewa "Ya Sunan Ki"? Sehrish dake tsaye agabansa idonta cike tab da kwalla duk ta tsorata murya na rawa tace "SEHRISH"

  Jinjina kai Abbansu yayi tare da sa hannun shi ya shafa gefen fuskar sehrish yace "Daga yau Ba sunanki Sehrish ba," 

  cikin mamaki suke kallon Abban nasu, itama sehrish É—in kallonsa take tana jira taji sunan daya canza mata, azmee kuwa Alhamdulillah kawai take faÉ—i aranta,

  "Kinsan menene sunan ki daga Yau"? abban nasu ya faÉ—i yana kallonta,

 Cikin sanyin murya Reesh tace "a'a".

   murmushi Abban nasu yayi sannan yace "daga Yau sunanki *SEHRISH SALAHUDDEEN HUSSEIN ABBAN SOJOJI*"

😇😇😇


Sakin baki su kayi suna kallon Abban nasu 


Duk wannan Abun dake faruwa akan idon SGR wanda ke saukowa down stairs jikinsa na sanye da t-shirt mai gajen hannu baÆ™a, sai dogon wando fari, sun bi shape É—in jikinsa ya fito Handsome  stylish É—insa, ya É—aure sumar nan ta baya ba Æ™aramin kyau yayi ba, a hankali yake tattaka steps É—in cikin tafiyar nan tasa ta majiya Æ™arfi, duk suka É—ago suna kallon shi................

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

__________________________________


    Ku hanzarta yin Payment don in na tashi dakatawa gaba É—aya  ne wanda suka shirya suyi mun magana direct = 08103884440

Post a Comment

0 Comments

Ads