```The father Of Soldiers```
Story
&
Written
By
Hafsat Bature
(Boss Lady)
◻ "To rasa kunya 6eran tanka zaka fara mun tsokanar taka ko,"?
◻ junaid yace "ae gaskiya na faÉ—a Abba, kallon ka kawai nake yi kai ta shan Æ™amshi kamar baka son momynmu alhalin ko rannan kana bacci cikin mafarki naji kana cewa bana ji bana gani ni makaho ne agame da sonki Momyn junaid in bake ba sai rijiya in na rasa ki zan rungumi transformer akanki zan iya tunkararrrr
◻ bai idasa ba saboda jin saukar pillow din da abban nasu ya wurgo mashi, tabbas junaid ya bawa abban nasu dariya sosai
◻ "Kai ko? Yaushe akai hakan junaid Ƙaraya kke mun," ya faÉ—i yana kara janyo Wani pillow ya wurga masa, hannu junaid yasanya ya ca6e pillow É—in da Abban nasu ya wurgo masa a Æ™injinsa ya rungumesa yana faÉ—in "thank u Abbana dole na gode maka domin gashi da hannunka ka miÆ™o mun juliet É—ita," ya faÉ—i hakan yana shafa filon dake Æ™irjinsa yayin da yake kallon fuskarshi cikin madubin gabansa,
◻ Jin shiru Abban nasu bai sake cewa komai ba, yasanya junaid juyowa da kallonsa, samun sa yayi zaune tsakiyar gadon kansa na kallon Æ™asa Allamar da damuwa a fuskarshi,
◻ tasowa junaid yayi jiki asanyayye ya haye saman gadon in da abban nasu yake yace "Abbana meya faru naga kashiga wani yanayi na damuwa,"?
◻ É—agowa Abban yayi ya kallesa cikin sanyin murya yace "Junaid momynku ! kasan bana 6oye maka komai kaine abokin sirrina, babu wanda ke fahimtar zuciyata kamar kai," ya dakata da maganar yana dan jinjina kai,
◻ "Dad pls tell me may be i ave the solution of it,"
◻ "Junaid mom É—inku ta azabtar dani da soyayyarta, junaid ita tace tana so na tun kafin na fara sonta, amma kalli ynx ta kama hanya da aure na akanta ta koma australlia da zama, junaid ya zanyi?
◻ gyara zama junaid yayi suna fuskantar juna kamar zaiyi maganar arziki sai cewa "Abba dole sai ita? Ga zankaÉ—a zankaÉ—an mata nan Æ´an goma shatakwas Æ´an shila kyawawan gaske masu neman sugar daddy irinka wlh abba har rububinka zasu yi ka share ta kawai ka auri wata," in serious matter junaid yake magana,
◻ Takaici ya hana abban magana a tunaninsa junaid zai bashi shawara akan yadda zasuyi mom É—insu ta dawo wurinsu da zama, amma sai ga akasin hakan, in banda sangartaccen irin junaid waye zaiso ayiwa uwarsa kishiya"
◻ "Abba u didnt say anything, shawarata batayi bane,?.
◻ "Eh junaid batayi ba, ashe baka da hankali in rasa wa zanyiwa kishiya sae momynku, bakasan halinta bane, duk da bamu tare da ita amma tayimun gargaÉ—in cewa muddin na Æ™ara aure sai ta dasa Bomb acikin gidan kowa ma ya rasa,"
◻ Fashewa da dariya junaid yayi, abban nasu yaci gaba da cewa "kuma in banda abunka wani magidanci ne mai Æ´a'Æ´a irinsu Sgr da Marshal Omar zai kara aure, auren ma Æ´ar shekara sha takwas ae wlh a ranar da ta sa Æ™afarta acikin gidan nan aranar zasu balla ta gutsi gutsi
◻ Dariya kawai junaid yake kwasa wato ta ko'ina ba sauÆ™i, ita mommy tace zata dasa bomb su kuma su Babban yaya in an kawo ta gidan 6arar gyaÉ—a zasu yi mata,.
◻ "Enough junaid dariyar ta isa haka, zan baka lokaci daga yau zuwa gobe kayi tunanin shawarar da zaka bani akan yadda zamu shawo kan momynku ta dawo nan da zama,"
◻ "Kana nufin muyi mata wayau abba,"?
◻ É—an zaro ido abban yayi tare da cewa "kai ! wannan matar mai É—an banzan wayau kamar dila tab ae banta6a ganin dakakkiyar mata ba irin momynku ae wannan ba wanda ya isa ya yayi mata wayau,
◻ Dariya su kayi gaba É—ayansu sun jima suna fira kafin su kwanta tare Abban yayi musu addu'a yabi ya shafe su duka,
◻ _____________________________________________
◻ Æ™aramar yarinya ce wadda bazata gaza shekara 12 ba ke tafama gudun saman titi sai faman kuka takeyi tana ambaton sunan "Oumma !! Oumma !!! ba tare da ta lura ba wata Æ™atuwar motar Æ™irar range rover tayi awon gaba da ita, nan take kanta ya fashe jini ya soma kwaranyo wa ta ko'ina
◻ A firgice sehrish ta farka daga mummunan mafarkin da take yi murya na rawa ta furta "Innalallahi wa'ina ilaihirraji'un," ta faÉ—i tana cusa hannunta cikin sumar kanta idonta sunyi jawur hawaye na bulbulowa daga cikinsu, tabbas ta tsorata da mafarkin da tayi,
◻ Jiki a mace ta tashi ta wuce toilet saboda lokacin sallama yayi, sai da ta watsa ruwa sannan ta É—aura alwala ta fito tana ta faman sauke ajiyar zuciya,
◻ Wardrobe ta buÉ—e ta dauko hijab É—inta ta shimfiÉ—a sallaya ta kabbara sallah, bayan ta kammala ta zauna saman sallayar ta É—aga hannayenta tana addu'o'i,
◻ Bayan ta kammala komawa tayi ta kwanta saman bed batare da ta cire hijab É—in ba, haÆ™iÆ™a mafarkin É—azu da tayi ya tuna mata wani abu mummuna daya ta6a faruwa makamancinsa,
◻ Ta jima hawaye na gangarowa daga eyes É—inta kafin wani baccin ya sake É—auke ta, ba ita ta farka ba har sae wurin Æ™arfe tara, jiki na rawa ta shirya kamar kullum ta wuce kitchen,
◻ tsayawa tayi tana zazzare ido ganin har azmee ta kammala breakfast É—in, wanda zata je ta jera a dining kawai take shiryawa,
◻ "Ina kwana aunty azmee," tayi maganar tana Æ´a kame kame, murmushi azmee tayi tare da cewa "Lafiya lou reesh, fatan kin tashi lpy,"
◻ "Aunty azmee ai mun afwa ban fito da wuri ba,"
◻ "Bakomai sehrish nifa da so samu ne ki koma kawai room É—inki na kawo miki breakfast É—inki ki ci acan ba sai kinyi wani aiki ba,"
◻ murmushi sehrish tayi tare da cewa "hakan bazaiyiyu ba auntyna, nima bana so nabar miki aiki dayawa ke kaÉ—ai,
◻ Sehrish tayi maganar tare da Æ™arasawa ciki domin ta taya azmee shirya abincin da zasu jera,
◻ Kamar daga sama ya faÉ—o kitchen É—in daga shi sai shorts ajikinsa ba riga,
◻ gaba É—ayansu sai da gabansu ya faÉ—i ganinsa kwatsam haka ba sallama,
◻ daker azmee ta iya cewa "wata sabon gani haroon yaushe ka dawo ne ? Amma dae saukar dare kayi ko,"? Ta tambaya tana kallon shi
◻ idasa shiga yayi yana sakin murmushi yace "Eh jiya da daddare na iso, nayi mamaki da banganki ba auntyna gaskiya i really missed u, nayi kewar delicious É—innan naki,
◻ da Æ´ar dariya a fuska azmee tace" ae yanzu tunda ka dawo sai ka dasa daga inda ka tsaya, halan yanzu ma yunwace ta koro ka,?
◻ "Eh auntyna fruits nake so da coffee haka ko tea, pls a shirya mun sannan abawa wannan mai aikin yakawo mun," yayi magana yana kallon sehrish wadda tunda ya shigo gabanta ke faÉ—uwa tarasa dalilin hakan,
◻ "Shikenan yanzu zan bashi ya kawo maka,"
◻ Murmushi ya saki tare da juyawa ya fuce daga kitchen É—in,
◻ "Wanene wannan aunty azmee"? Sehrish ta tambaya domin neman Æ™arin bayani akansa,
◻ Azmee tace "Wannan haroon kenan, ki saki jiki dashi bai da wata matsala a iya sani na, shima É—ayane daga cikin matasan gidan nan,"
◻ É—an ta6e baki sehrish tayi tare da jinjina kai tace " Allah yasa bai da wata matsala," aranta kuma tace "sam ni baiyi mun kama da sauran ba, hasalima duk sun fishi kyau da natsuwa,"
◻ Ba da son ranta ba azmee ta shirya mata fruit a tray da cup na coffee takai masa,
◻ sai da tabi kwatancen da azmee tayi mata sannan ta gano room É—insa a nan down yake kusa dana kanal yusif,"
◻ a bude tasamu kopan sallama ta kwala masa daga ciki taji ance "Come in,"
◻ Shiga ciki tayi gabanta na faÉ—uwa rass rass, daga kwance yake saman haÉ—aÉ—É—en gadonsa ya taso zaune yana Æ™are mata kallo,
◻ Cike da girmamawa sehrish tace "Gm sir,"
◻ bai amsa mata ba har ta ajiye masa fruits É—in asaman table É—in dake a front É—insa,
◻ Cikin sauri tajuya zata fita muryarsa ta katse ta"na sallame ka ne,"? Jiki a mace ta dawo ta tsaya daga tsaye tare da sunnar dakai tana kallon yatsun hanunta da take wasa dasu,
◻ Jin shiru yasa ta É—an dago ta kallesa samun shi tayi yana bin jikinta da wani irin matsiyacin kallo tundaga kan yatsun Æ™afarta har izuwa Æ™irjinta,
◻ Hankalinta ba Æ™aramin tashi yayi ba, ita burinta ya sallame ta tawuce taje wurin dining don ta taya aunty azmee ga kuma son sanya Babban yaya da take yi a idonta,
◻ Ganin ya tsayar da idonsa a gaban wandon jikinta yasanya tsigar jikinta tashi,
◻ da buÉ—ar bakinsa sai cewa yayi "ina Ak47 É—inka take, don ni banga alamarta ba anan,"?
◻ Cike da rashin farintar me yake nufi sehrish tace "bangane me kke nufi ba,"
◻ Wani shu'umin murnushi haroon ya saki tare da kai hannu cikin tray É—in da takawo masa ya É—auko damin Banana ya cire guda tare da sa hannu yana 6are bawon ayabar yace "Ina nufin wannan," yayi nuni da ayabar dake hannunsa,.
◻ Jigum sehrish tayi sam tagaza fahimtar me haroon ke nufi, ganin bata da niyar bashi amsa yasa shi cewa "ina nufin abu na maza wannan," yayi maganar yana ruÆ™o abunsa dake cikin shorts É—in jikinsa,.
◻ Zaro ido sehrish tayi gabanta na faÉ—uwa zuciyarta tayi mugun tashi ganin abunda yake nuna mata sai lokacin ta gane me yake nufi ma,
◻ Shiru tayi idonta na kallon Æ™asa gabanta na faÉ—uwa
◻ "A cire mun wando inaso nagani na shaida,"
◻ Ya faÉ—i ayayin da yake kai ayabar hannunsaa cikin bakinsa yana gatsa yana ci,
◻ Ji tayi gaba É—aya komai ya tsaya mata tsak, tabbas ta tsorata da haroon sosae tun da take aiki a gidan bawanda ya ta6a lura da hakan farat É—aya sai shi,
◻ "Baza a cire ba,!? ya tambaya a fusace
◻ Cikin en ena sehrish tace "kayi hkr dan Allah ! amma baxan iya yin abunda kke so ba......," kafin ta idasa maganar tuni yasanya hanunshi yaja zariyar wandonta nan take wandon ya tafi suuuuuuuuuu zai sabule jiki na rawa ta cafko shi tayi saurin maidashi ta É—aure abunta a yayin da zufa ke wanko mata,
◻ Dariya haroon yayi kafin ya tsagaita yace "Ke !!! nifa tun jiya dana ganki nasan cewa Ke maca ce ba namiji ba !!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!
◻ É—agowa da ido sehrish tayi a firgice tana kallonsa tamkar a mafarki take jin kalaman haroon .
◻ Ƙara jaddada mata yayi da cewa "Ke maca ce ba namiji ba !! ki faÉ—amin uban miyasa kikayi shigar namiji kika zo gidannan? Da kwai wata manufa aranki ko !!?
◻ Muryar na rawa sehrish tace "innalallahi wa'inna ilaihirraji'una!! taya akai ka gane cewa Ni maca ce farat É—aya!?
◻ Dariya haroon yayi tare da cewa "saboda ni Shu'umi ne ! Kuma cikakken É—an duniya wanda idonsa ya buÉ—e a harkar barikanci ! ba wani abu da mutun zai 6oye mun batare dana gano sa ba,"
◻ "Shikenan nashiga ukuna !! dan Allah ka rufemun asiri karka ce zaka tona cewa ni maca ce pls!!
◻ Ajiye ayabar dake hannunsa yayi cikin tray É—in sannan yace "Okey, i won't expose ur secret but under one condition!!?.
◻ Ya faÉ—i yana kallonta a raunane sehrish tace "koma meye zanyi nidai karka tona mun asiri," tuni idonta ya ciko tab da kwalla,
◻ Har wani lumshe ido haroon yake yi yana kallonta " share hawayenki baby, bani da matsala muddin za'a biyamun buÆ™atata,'
◻ shiru sehrish tayi tana sauraron shi
◻ "Zamuyi magana anjima yanzu zaki iya tafiya naga kuna cikin aiki ne,"
◻ tunkan ya idasa mgnr sehrish ta fuce tana shasshekar kuka ,
◻ sai da ta dakata bayan ta fita ta tsaya ta share hawayenta tare da dai dai ta natsuwarta sannan ta sauka Æ™asa, anan ta samu ma Aunty azmeen tana jera musu breakfast É—in a dining,
◻ Karasawa tayi suka ji gaba da jerawa atare,
◻ Kallonta azmee tayi tare da cewa "Naga kin jima ! Lapiya dae ko?
◻ "Eh," ta bata amsa atakaice, ita kaÉ—ae tasan yadda take ji aranta, brain É—inta ta gama shiga ruÉ—u tashiga tashin hankali mamakinta taya akai farat É—aya haroon ya gane cewa ita maca ce !? how many days ta share a gidan amma ba wanda ya ta6a lura in aka cire junaid sai shi wanda jiya jiyan nan yazo da daddare, tabbas abun ya É—aure mata kai, kuma tasa mishi alamar tambaya, (?) Anya ba Aljani bane
◻ gaba É—aya ta tafi duniyar tunani har batasan cewa masu gidan duk sun fito ba, domin yin breakfast, yawancinsu duk jallabiya ce ajikinsu,
◻ Fawan da twins ne suka fara hallara suka zauna a kusa da juna, sai Irfan da jabeer bayansu sai khaleed da kanal yusif, duk suka gaishe da Azmee ta amsa musu kafin ta ci gaba da saving É—insu,
◻ Har time É—in sehrish bata cikin hayyacinta tana tsaye kamar gunki tana tunane tunane iri iri aranta, sam azmee bata lura da halin da take ciki ba,
◻ A tare Abbansu ya fito da baby junaid hannunsu cikin na juna, fuskar nan tasa a washe tun da idonsa su kayi Arba da sehrish É—insa, tunkan ya Æ™araso ya lura da cewa ta tafi duniyar tunani,
◻ Ganin Abbansu yasa suka haÉ—a baki wurin gaishe shi "Barka da safiya Abba, kun tashi lafiya,"
◻ "Alhamdulillah My Sons ina fata kuma kuna lafiya,"
◻ da fara' a fuskan kowannansu suka amsa mishi,
◻ Bayan sun zauna cike da tsokana junaid yace
◻ "Ni bazaku gaishe ni ba"? ya faÉ—i yana kallonsu,
◻ Tsoki fawan yaja tare da cewa "kabari sai ka fara ajiye gemu da Æ´a'Æ´a tukunna,
◻ "Wai junaid da gemu ba rana ba wata, don gsky ban ga alamar junaid zai yi gemu ba ko nan gaba,'
◻ Acewar Jahan,
◻ Abbansu yace "Talle zatai wa audu gori, ka fara duba fuskarka tukunna, muddin junaid bazaiyi gashin baki ba ko na gemu to kaima haka baza ta6a yi ba,"
◻ dariya su kayi gaba É—ayansu kanal yousuf yace "Wai ina Haroon ne ? Shi bazai fito bane?
◻ Abba yace "taya zai fito bayan abunda ku kayi masa jiya, sam banji daÉ—i ba, tun da ya dawo ya kamata ku tarbi É—an uwanku hannu bibbiyu, in baku ja shi ajiki ba taya zai shiryu ? Yayi maganar cike da nuna 6acin rai akan abunda su kayi jiya,
◻ "Abba amma ba ka ga irin yadda yake mana magana ba har agabanka batare da jin komai ba? Acewar Irfan,
◻ Ajiye cokalin dake hannunsa yayi tare da cewa " in da sabo ae ya isa ace kun saba da halinsa, addu'a kawai zaku bishi da ita Allah ya shirye shi," yana kai karshen maganar ya É—auki spoon É—in yaci gaba da cin abincin dake gabansa,
◻ Jinjina kai su kayi kawai shikam fawan ta6e baki yayi tare da cewa "Ashe dagaske yazo, ae ni nayi tunanin duk mafarki ne zuwan nasa jiya,"
◻ Harararsa khaleed yayi "dole kace haka dama bakwa good time dashi ae,"
◻ tun da suka ambaci sunan HAROON hankalin sehrish ya dawo jikinta, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi ga zufa na wanko mata,
aza idonta tayi akan junaid wanda ke ta faman satar kallonta yana mata murmushi
◻ Murmushi itama tasakar mishi,
◻ So yake yayi mata magana amma ba hali sai dae daga inda yake ya rinÆ™a yi mata alama da bakinsa batare da sauti ya fita ba yace "Sehrish kin tashi lafiya,"
◻ tagane me yake cewa don haka itama tayi kamar yadda yayi tace "lafiya lou junaid ina fata kaima haka,"
◻ É—aga mata kai yayi alamar eh, duk abunda junaid keyi akan idon Abbansu mamaki yake menene tsakanin junaid da mai aikin nan tukur, kodae sun Æ™ulla abota ne, É—an murmushi ya saki domin yaji daÉ—in hakan, sbd duk wani abu da zai sanya shalelensa farin ciki son shi yake,
◻ "Ga babban yaya nan fa kowa ya shiga taitayinsa" fawan ne yayi maganar a yayin da yake cunkusa kebab abakinsa,
◻ Yadda fawan yayi maganar yasanya abbansu yin dariya, wai ga babban yayanan kowa yashiga taitayinsa, Kanal yusif yace "wato kaine annoucer duk in big bro zai fito sai kace kowa ya shiga taitayinsa, nawa ake biyanka salary ne ?
◻ Dariya sukayi gaba É—ayansu cikin nishaÉ—i in ka cire Twins dake ta faman jin bugun zuciya,
◻ A tare suka fito su biyu shi yana saukowa daga saman stairs yayin da shi kuma Haroon ke fitowa daga part É—insu dake a nan down,
◻ Jikinsa na sanye da tank top riga ce kamar singlet haka take fara, sai wando jeans, sumar nan tasha gyara,
◻ Shi kuma Haroon shirt ce da gajeran wando ajikinsa, ga uban gashin jiki da Allah yayi masa don ma Allah yasa kwantacce ne amma duk da haka ba kyan gani,
◻ Ganin Sgr yasa shi fara yi mashi kirari "Barka da Fitowa Babban yayanmu Namijin Zaki Uban dawa, mai mulkar Æ™ananun Æ´an iska kai É—aya tak kake tada runduna, gabanka Bullet bayanka Bomb ka ga Ingarmar Namiji Æ™asaitacce takawarka lafiya Namijin duniya,'
◻ wannan kirarin na haroon yasa su Yousouf dariya, shi kuwa Sgr ko kallo haroon bai ishe shi ba,
◻ A tare suka Æ™arasa ya zauna a empty chair É—in dake kusa da Junaid, haroon ma yasamu wuri ya zauna,
◻ "Barka da safiya Abbana abun alfaharina,"
◻ Murmushi Abba yayi tare da cewa "Yawwa barka dae Haroon ya gajiyar tafiya ?
◻ "Abba ae ta washe tun jiya, yanzu garass nake jina,"
◻ Jinjina kai Abba yayi tare da cewa "Naji kace ka Æ™aro wulaÆ™anci dagaske ne?
◻ Cikin sauri haroon ya saci kallon Babban yayan nasu yace "Bana cikin hayyacina ne, shiyasanya nayi maganar,"
◻ Murmushi su kayi gaba É—ayansu,bayan nan suka shiga gaishe da babban yayan nasu, bai amsa ba sai dai ya rinÆ™a yi musu alamar yaji da kansa, gyaran murya abbansu yayi hakan yasa Sgr É—agowa ya kallesa cikin sanyin murya yace "Gm Dad,"
ta6e baki Abba yayi tare da cewa "sai ynx ka ganni? Ni fa narasa ganewa, nan gaba ina ga sai na rinƙa gaishe ka dakaina da alama,
"Insha Allah hakan bazata ta6a faruwa," sgr yayi maganar ayayin da yaÉ—auke idonsa daga nakan Abban, Murmushi Abban yayi, yarasa dalilin dayasanya yake jinshi sosae aransa ko dan yana kama da Momynsa alexandra,
Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
Sehrish kuwa
◻ Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta time É—in da tayi arba da kyakkyawar fuskar Sgr duk da a firgice take ganin yadda haroon ke satar kallonta,
◻ tunkan azmee tayi yunkurin zuba mishi breakfast É—insa sehrish ta riga ta, plate ta É—auka ta zuba mishi Chips ta shake mashi shi, sannan ta tura mishi agabansa ta kuma haÉ—a masa da hot coffee a acikin cup,
◻ "Mlm tukur ni baza'a zuba min bane"? Haroon ne yayi mata maganar yana binta da wani irin shu'umin kallo,
◻ Jiki na rawa sehrish ta É—auki plate hannunta har kerma yake yi, tama rasa me zata zuba mishi,
◻ Muryarshi ce ta katse ta da cewa "Snacks nake so",
Cikin sauri sauri ta zuba mishi snacks É—in sannan ta haÉ—a masa da lemu a cup ta tura mishi,
◻ "Yawwa Good Job," ya faÉ—i yana kai hannunsa cikin plate É—in ya É—auki donuts yakai bakinsa,'
◻ matsawa tayi daga bayan sgr ta tsaya saboda ta
◻ samu damar da zata rinÆ™a kallon sumar kanshi da kyau, tana shakar turaren shi,
◻ Ji take tamkar takai hannunta ta shafi sumar nan tashi, tun da ta tsaya abayan sgr bata motsa ba, duk wanda ya faÉ—i yana buÆ™atar wani abu sai dae azmee ta zuba mishi, ita kawai Babban yaya take saving abunda yake so,
◻ É—agowa junaid yayi da idonsa ya É—an kalle ta dayake tana tsaye daga bayansu, mamaki ne ya kamashi ganin yadda sehrish ke ta faman kallon Babban yayan nasu ko kyaftawa batayi, sam bai kawo wa ransa komai ba game da kallon nata kawai yasanwa ransa cewa wata'Æ™il respecting ne yasanya sehrish tsayawa abayan, kallonsa kuma da take yi may be burgeta yayi ne, amma yaso ace shi sehrish take ma wannan kallon dayaji daÉ—i, mayar da kansa yayi jikinsa a sanyaye yaci gaba da shan farfesun naman dake gabansa cikin plate,
◻ Sun jima suna É—awainiyar zuba musu breakfast É—insu kafin daga bisani kowa ya fuce, banda junaid da haroon suna acikin gidan, Sgr sun fita tare da abbansu headquater
_______________________________________________
A 6angaren su Hosana kuwa Tun da asuba da saude ta tashe su su kayi salla, suka koma tare da shimfiɗa wani sabon baccin kamar matattu haka suka dingi sharar bacci, dole kuyi bacci Allah, zaman cell ba daɗi anjima ana cikin tashin hankali, ga sauƙi yazo daga Lillahi,
Koma wa kitchen saude tayi ta shiga harhaÉ—a kayan breakfast da zatayi amfani dashi, shaf shaf ta fere dankali turawa bayan ta kammala ta yanka shi slide sannan ta shiga soya shi a saman frying fan,
Muryar goggo ce ta katse ta da cewa "umm agogo sarkin aiki nace ya akai banga yaran nan ba? Kodai mafarki nayi jiya?
Fuska É—auke da dariya saude tace "Su wa kike nufi kenan"?
Watsa hannu tayi tare da cewa "Ƴa'ƴan Abusufyan mana? waɗannan tagwayen ?
ta tambaya tana neman jin ƙarin bayani,
Bin ta da kallo saude tayi jikinta na sanye da kayan baccin nan ƴan gado, sun yamutse sun tsufa riga da wando kwalar rigar ta sukurkuce, gasu Over size sun mata yawa kamar agwagwa haka ta koma acikinsu, taƙi ta janza wasu koda yaushe akayi mata magana akan ta sauya wasu kayan baccin sai tace tafi son waɗannan saboda ƴan ƙasar turƙiya ne irin wanda Zehra ke sanya abarmata abunta, wato ta cikin tarkon kauna, Abusufyan ne yayi mata tsarabar su tun last year dayazo nageria,
Gashi ta ƙife ɗan kwalin atamfa akanta abundae ba'ace wa komai,
"Saude kinyi shiru baki ce mun komai,"
daker saude ta iya cewa "Suna nan mana, ba mafarki kikayi ba goggo, suna can suna sharar bacci É—akina,
Washe baki goggon katsina tayi tare da cewa "Yawwa madalla har hankali na ya kwanta," ta faɗi tana shafa saitin zuciyarta, hakan ba ƙaramin sa saude dariya yyi ba,
goggo taci gaba da cewa "Saude so nake ki shirya musu karin kumallonsu mai daɗin gaske, a shaƙe musu tray, sannan a hada musu farfesun kaji dan Allah naga ƙasusuwan wuyansu kamar an jera ƙarafuna suna fama da yunwa, so nake kafin Abusufyan yadawo daga ƙasar turƙiya ko ina na jikinsu ya cicciko suyi kyau ƴan dumur-mur,' tayi maganar tana kwatanta yadda take so su koma da hannunta,
Dariya kawai saude ke saki jin abunda goggon tace wato ƙashin wuyansu kamar an jera ƙarafuna, har dafe ciki take yi,
"Bansan iya shege wa kike wa dariya? Saude kin raina ni ko ina magana kina mun dariya, idan kika fusata ni, yau yau É—innan zakiyi fiffige ki koma rugarku acigaba da kiwon shanu,"
Tsuke fuska saude tayi jin abunda goggo tace rai abace tace"shikenan tun da haka kke so bari naje na shirya kayana yau dai na tafi na huta da gori," tayi maganar tare da kama hanya zata bar kitchen É—in, .
Da sauri goggo ta ruƙo hannunta fuska dauke da murmushi cikin lallami tace "haba ƴar saude ta ke ko bakisan wasa ba, in kika tafi wa zai haɗawa ƴa'ƴan abusufyan ɗina breakfast ɗinsu,"
Murmushi saude tasaki ganin yadda goggo ke lallashinta yau, ita tasan saboda twins É—incan tasamu wannan kulawar,
Koma cikin kitchen É—in tayi tana cewa " shikenan na fasa, amma goggo gsky ki barni nayi aikina mana, kinzo sai katse ni kike yi,"
Juyawa goggo tayi ta fi ce tana cewa "To natafi Allah baki haƙuri, ayi aiki lafiya,
Sai da goggon katsina ta wuce ɗakin saude ta tura kopan ɗakin ta hangi su Hosana da Jahad suna bacci sannan hankalinta ya kwanta hada jinjina kai da cewa "Masha Allah, ƴa'ƴan abusufyan ɗina kusha baccin ku ku more ƴan gatana abinci na nan yana jiran ku," ta kammala sambatun nata sannan ta koma falo ta kunna kallo ta samu wuri ta zauna saman 3 seater tana cewa "Oh ko yaushe suke maimaicin shirin Omaru da zahra, aiko bari waɗancan yaran su tashi daga bacci in nuna musu ƙasar da mahaifinsu ke zaune, ni nasan ma ba'a rasa ganin shi acikin film ɗin wata'kil ko yazo giftawa aciki Camera man ya hasko dashi,"
Haka ta runka sambatu ita kadae abunta, sam bakinta bai zama hakannan batare da tace wani abu,
Bayan saude ta kammala breakfast É—in, acikin katon tray ta jera warmers É—in da sauran food stuffs É—in ta shigo falon dasu,
Tunkan ta karaso goggo tace "Yawwa saude na maza ajiye shi anan gabana, sannan kije ki tasomun ƴa'ƴan Abusufyan ɗina, bayin Allah suna can suna fama da yunwa, bacci bai da imani baisan in kana jin yunwa ba ya ƙyale ka ba,"
Fashewa da dariya saude tayi aranta tana cewa wato da ace goggo ƴar comedy ce ba ƙaramin nishaɗantarwa zatayi ba,
Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
Ajiye tray ɗin tayi asaman carpet ɗin geben ƙafar goggon kamar yadda tae commanding ɗinta, sannan ta wuce room.ɗin ta don ta tayar dasu Hosana da Jahad,
Duk wannan abun dake faruwa Goggo da saude basusan cewa Omar da Babban likita suna cikin gidan ba, saboda dama jiya bayan sunyi bacci suka dawo, Su hosana ne kawai suka sani saboda sunyi magana dashi,
duk in taga yaran wani farin ciki take ji aranta, sai faman sharar baccinsu suke, addu'arta Allah yasa Yaya Omar yabar musu twins É—in su zauna agidan koba komai zata samu abokan fira,
Ƙarasawa tayi gaban gadon ta sanya hannunta ta ɗan bubbugi ƙafafunsu a hankali kamar wadda zata tasar da Jarirai,
Farkawa su kayi kowa na faman yin hamma, atare suka tashi zaune suna kallonta, lokacin da jahad ta shaida ta cikin sauri tace "ina kwana Aunty," murmushi saude tasaki tare da cewa "Lpy lou my sisters fatan kun tashi cikin ƙoshin lpy,"
Jahad tace "Alhamdulillah aunty, munji daÉ—i sosai da kulawarnan,
"Aunty nidai Yunwa nake ji, da yunwa natashi kamar na cinye ƴan hanjin ciki na," hosana ce tayi maganar, fashewa da dariya saude tayi hada jahad ɗin, murya a ƙule Jahad tace "waike baki da kawaici ne? Ko gaishe ta bakiyi ba sai magana akan yunwa yunwa,"
Murmushi saude tayi tare da cewa"kwantar da hankalin ki, special breakfast na nan nayi maku reserving É—inshi a palor, kuma goggonku na nan tana jiran ku, sai tambaya take ina Æ´a'Æ´an abusufyan É—inta,"
Jin hakan yasa su yin murmushi tare da kallon juna, kafin jahad tace"Aunty saude dama ina so na faɗamiki jiya yaya Omar yazo munyi magana dashi har yace mana, mu shirya yau zai wuce damu kaduna gidan yayan shi, gsky mun fi so muzauna anan," ta ƙarasa magar tana kallon sauden,
dafe ƙirji saude tayi tare da cewa "Wai dagaske abunda ya faɗamaku kenan ! Hakan na nufin bazai bar mana ku nan ba, mu zauna atare ya Allah,' sam bataji daɗin hakan ba, har cikin ranta, babban tashin hankalin ma da taji Jahad tace zai kaisu kd gidan Yaya ishaq,
Aranta tace "tabɗijan gidan wannan shu'wa arab ɗin jarababbiya, sam bana fata akai yaran nan can saboda bazata ƙyalesu ba, sai ta azabtar dasu waiyo Allah na, ya zanyi yaya omar yabar mana su anan su zauna, wlh aunty babba bata da mutunci ga Hafsat kuma yadda yarinyar nan ta tsani talaka aikom yaya omar zaiyi gangancin jefa rayuwarku cikin hadari,'
"Aunty baki ce komai ba? dan Allah kice masa yabarmu anan muzauna daku munfi jin daÉ—i," jahad ce ta katse mata tunanin da take yi,
Jiki a mace saude tace "i dont know wat to do, yaya omar in yayi niyar yin abu no body can stops him, kuyi addu'a kawai Allah yasa goggo ta hana shi tafiya daku, amma muddin aka kaiku gidan yaya Ishaq kun shiga uku,"
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba jin abunda saude tace, murya na rawa jahad tace "aunty meyasa kika ce haka"?
Saude tace "hmmm abar zancen kawai, ku tashi ynx ga breakfast can na jiranku, ga goggo kuma nasan ganinku, ni ynx kitchen zan koma na shiryawa su yaya Omar nasu, pls kusan yadda zakuyi kar yaya Omar yabar gidan nan daku," tana gama faÉ—an hakan ta fice izuwa kitchen zuciyarta nayi mata ba daÉ—i saboda tausayin yaran duk da batasa su wanene su ba amma tasan basu da gata, yaya Omar kuma dama shi mutun ne mai son taimakai wata'kil wani wuri yagansu a wahalce yake son taimakon rayuwarsu, da wannan tunanin Saude ta shige kitchen,
Kallon juna su kayi cikin tsananin tsoran inda za'a kaisu, atare suka tashi haryanzu doguwar rigar material É—innan ce ajikinsu, mayafi kawai suka É—aura akansu sannan suka fito,
Goggo naganinsu ta soma washe baki tana cewa "masha Allah Æ´a'Æ´an abusufyan É—ina maza ku matso ku kwashi albarka wurin gaggonku, ga kuma abincinku na jiranku,"
Da fara'a suka karasa atare suka zauna suna gaishe ta "barka da safiya goggonmu fatan kun tashi lafiya,"
"Lafiya lou Alhamdulillah, har mafarkin ku saida nayi jira, tsorona kar na farka na taras da bakwanan agidan bansan ya zanyi ba, in banga Æ´a'Æ´an abusufyan É—ina ba,"
fuskarsu cike da tsantsar farin ciki ga kaunar goggon katsina data shiga ransu daga jiya izuwa yau,"
"Yawwa maza ga shinan kuci ku ƙoshi, in ma bai isa ba aƙaro maku,"
Cike da zumuɗi hosana ta ɗauki plate ta bude warmer ɗin dake ɗauke da soyayyan dankalin turawa ta shake plate ɗin dashi, sannan ta bude ƙaramar kular jar miya ta lafta asama, ta motse ta shiga da turama cikinta,
Jahad kuwa Wainar kwai ta rinƙa haɗawa da slide bread tana cunkusawa abakinta, hannu goggo tasanya ta ɗauki flask ɗin dake ɗauke da ruwan liptop, ta tsaiyaya musu a cup kowa da nasa sannan tace "ga madara nan leda kowa ya zuba yadda zata ishe shi,"
Zame hannu hosana tayi daga irishi É—in da take ji don haÉ—ama, ta É—auki milk É—in ta zazzafa acikin ruwn tea É—in mai uban yawa, tana jin jahad na cewa "banza kaÉ—an zaki zuba,"
Harara ta watsa mata tare da cewa "ina ruwanki ! ki ci abunda ke gabanki," sai da taga ruwan tea É—in yayi kauri yaji uwar madara sannan ta tsagaita ta sanya sugar," ta hada tana sipping É—inshi,
girgiza kai kawai jahad tayi tare da haÉ—a nata tea É—in tashiga kurbarshi tana ci da bread É—in,"
Kamar kura haka ta lamushe abunda ta zuma sannan ta bude warmer É—in dake dauke da chicken pper soup, ganin lafiyayyiyar kaza yasa hosana gyara zama, anjima ba'a haÉ—uwa hannunta har kerma yake yi wurin daukar cinyar kazar tana turawa abakinta, gwanin daÉ—i kunnanta har rawa sukeyi,
Goggo sai murmushi takeyi tana kallonsu tsananin ƙaunar yaran take ji har cikin ranta,
Jahad kam kunyar abunda hosana keyi take ji kamar ta shaƙo ta take ji, sai faman licking hands ɗinta take kamar mayya,
Ƙasa ƙasa da murya tayi cike da jan faɗa tace "su hosana basaban ba, gida babu makwabta babu gidan miji ba tabbas, banza tasamu sai wankarta ake ba baka sai kunne,"
Fashewa da dariya su kayi gaba ɗayansu, ashe goggo na jinsu sai cewa tayi "Inji wa ya faɗi maki cewa gida babu, tab Ke ko kinsan katafaren gidan da abusufyan yake rayuwa acikinsa acan ƙasar Turƙiya? Kinsan irin daukar dayake ciki ? ae wannan bakomai bane, hmmm lokacin da naje turƙiya nakai masa ziyara, in zan ci abinci saiya sa an jera mun kayan maƙwalashe cike da dining tabur ae masu aiki gare shi sun iya girki sosai in sukayi abinci kamar abincin Aljanna don daɗi," ta ƙare maganar tana jaddada musu mgnrta
Tsagaitawa da cin abincin su kayi suna sauraronta baki asake, sukam wai wanene wannan abusufyan É—in da Goggon katsina ke ta faman labarta musu zancen shi?
Kallon juna su kayi alamar neman karin bayani, goggo tace "ae ku kwantar da hankalinku, ni da kaina zansa abusufyan yazo nigeria ƙafarsa ƙafarku baxan ƙara bari ya tafi yabar yaransa cikin wahala ba,"
Sunnar dakansu su kayi ga dariya na cinsu, jin yadda goggo ke ƙaƙaba musu mutumin da basu san da Existing ɗinsa ba a duniya,
Atare Omar ya fito shi da babban likita sun shirya tsaf,
Goggon na ganinsu tace "Kai dirar yaushe ? ta ina kuka shigo cikin gidan,"
Murmushi Omar yasaki tare da cewa "goggona ke nan, ae jiya muka dawo tare da mutumina, mun same ku kuna bacci,"
Babban likita yace "Barkanka da safiya Mommyna fatan kun tashi lpy' yayi maganar ayayin da yake zama saman 2 seater, shi kuma marshal Omar ya samu wuri gefen gaggo yazauna saboda ya samu damar gaisawa dasu Hosana dakyau,
Atare suka haÉ—a baki wurin cewa "Barka da safiya yaya Omar dafatan ka tashi lpy," .
"Lafiya Alhamdulillah," ya amsa musu yana mai ƙara azan idonshi akansu," ba ƙaramin daɗi yaji ba ganinsu suna cin abinci,"
Duk kunya ta kama jahad har takasa idasa cin abincin, ita kuwa hosana bakin nan nata dama dama da jar miya, kuma a haka take kallonsa tana sakar mashi murmushi,
Bayan sun gaggaisa da goggo tace "daÉ—a sai naga Æ´a'Æ´an abusufyan jiya, ance wai kai ka kawo su naita mamaki nace yanzu har yaran nan sunyi girma haka amma ba'a ta6a nuna musu gidan goggonsu ba sunzo sun gaishe ni,'? Tayi tambayar rai a É—an 6ace tana kallon Omar,
Jim omar yayi yana kallonta cikin mamaki yace "Suwa kenan"? Goggo ta nuna su hosana tare da cewa "gasu nan mana,"
É—an murmushi yayi tare da kallon babban likita wanda shima murmushin ne a fuskarshi, sarai sunsan rigimarta, in ba haka ba yaushe Uncle Abusufyan ya ta6a aure balle har aje ga maganar aure,
Babban likita yace "Mommyna ayi mana afwan laifin mu ne, da bamu kawo su ba, kuma hada ƙarin makaranta sukeyi ne boarding school shiyasanya,"
ta6e baki goggo tayi tare da cewa "amma dae nikam ba'a kyautamun ba Allah, yara har sun isa aure amma ban ta6a sasu a idona ba! koda yake ba laifinku bane laifin Sufyanu É—inne zan hadu dashi sai yayimun bayanin yadda ya hana ni jinina,
babban likita yace "Mommyna kenan, ina fata kina shan maganinki da na baki akai akai? Yayi maganar yana kallonta,
Yamutsa fuska tayi tare da cewa "kai ni na manta da wasu magunguna, suna nan cikin kwandon shara nake zuba su, ai naji sauƙi ynx,"
dariya su kayi gaba ɗayansu hada su hosana, Omar yace "goggo ina fa sauƙi a nan? U need a medicine 4 ur health,"
"Ae narasa meke damun mommyna, magani mai tsada kike zubawa cikin dustbin, gsky bana jin daÉ—i,"
Tsuke fuska goggo tayi tare da cewa "nifa bansan Iya shege, lafiyata ce ko lafiyarku ? ta tambaya tana harararsu
babban likita yace "lafiyarki ae tamuce mommyna, samun lafiyarki ae shine kwanciyar hankalin mu,"
Omar yace "maganarka gsky ne bro, goggonmu ataimaka adaina zuba magani a dustbin pls yakamata kina sha,"
Murmushi tasaki jin yadda suka damu da ita tace "shikenan, naji zan rinƙa sha daga ynx,"
Bayan sun É—an tsagaita na wani lokaci Omar yace "goggo ina fata sun sanar dake cewa atare yau zan wuce dasu kaduna gidan yaya ishaq,"
Zumbur goggo tayi ta miƙe hankali atashe tace "bangane me kke nufi ba Omar? dama ba abusufyan bane yace akawo munsu nan ba su zauna wurina ? Bansan shegentaka fa ? Rabani zakuyi dasu ?
shiru Omar yayi just speechless ya ma rasa amsar da zai bata,
Babban likita ne yace "goggo go back to ur seat, lemme explain to u"
tsoki taja tare da cewa "Nifa bana gane ko wane yare a yanzu, in zakayimun magana da hausa kamun," tayi maganar tare komawa ta zauna don sarai taji mai yace, tsohuwar Æ´ar boko ce ,"
Æ´ar dariya dr haris yayi kafin yace "mommyna kin gane, yaran nan school suke yi acan, kuma exam suke zana wa, shiyasan ya muke so mu maida su makaranta kar asamu matsala,"
juya masa ƙeya goggo tayi tare da cewa "In ansan exam sukeyi a makaranta maiyasa to aka kawo munsu ? Don aja mun rai ! I hate nonsense wlh,'
Yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya ta basu ba gaba ɗayansu, hatta saude dake tsaye a ƙopan kitchen tana sauraran firar tasu sai da ta dara, jikinta duk yayi sanyi Allah Allah take aranta Allah yasa kada goggo ta amince akai yaran nan kaduna gidan Aunty Babba,"
Atare da Omar suka shiga lallashinta don ta amince, sam taƙi yarda har sai da dr Haris babban likita yace "mommyna i promise u da sun samu hutun school zansa akawo mana su nan, su zauna wurinki ko ba haka ba Omar? Yayi maganar yana kallon omar,
Marshal Omar yace "Yeah hakane, dakaina zansa akawo su goggona,"
jiki asanyaye gaggo tace "shikenan na amince amma karku sa6a Alƙwari da zarar ansamu hutu akawominsu in ba haka ba zan sanarwa Abusufyan ɗina,"
Murmushi suka saki atare kafin Omar yace "insha Allah, ' sannan ya kalli su hosana ganin sun kammala cin abincin harsun wanke hannayansu yasa shi cewa "Kuje ku shirya,"
Atare suka miƙe sam basu so zasu rabu da gaggon su da aunty saude, har sun fara tafiya jahad ta dawo zata ɗauki kayan abincin da suka ci Marshal Omar yace "just leave it, bari saude tazo ta kwashe,"
Juyawa tayi suka wuce bedroom ɗin saude suna shesshekar kuka, har cikin ransu basu son rabuwa da gaggonsu da aunty saude jiya izuwa yau sunji tsananin ƙaunar kasancewa dasu,"
Shaf shaf jahad ta fara yin wanka sannan hosana tayi, dukansu suna É—aure da towel suna shafa mai ajikinsu,"
Hannu tasa da sauri jin hawaye a idonta, goge su tayi da sauri, sannan ta gyara natsuwarta, ta shirya musu breakfast É—insu ta shigo da shi palor,
Bin ta kallo dr haris yayi tare da cewa "Omar ga fa future wife É—ina danake baka labari," .
É—an kallonta Omar yayi tare da cewa "Oh dama ita ce kenan, ni bansan ta ba,"
Dr haris yace "taya xa'ae kasanta, daga rugar fulani nazo da ita, amatsayin wadda zan aura don na nunawa goggonku amma goggo ta maida mun mata Æ´ar aiki, "
murmushi omar yayi batare da cewa komai ba, goggon kam tuni ta wuce É—akinta saboda rashin jin daÉ—i za'a tafi da Æ´a'Æ´an abusufyan É—inta
Saude jiki amace ta gaishe su, suka amsa sannan ta ajiye musu tray É—in, sannan ta juya ta kwashe kayan abincin da su hosana suka kammala dashi ta zuba a tray É—in ta wuce kitchen, bayan ta ajiye kayan ta koma É—akinta wurin su hosana, ko ido batasan ta haÉ—a dasu saboda kukan da take ji, saboda turken wawa,
Wardrobe ta buɗe ta ɗauko musu kayan da zasu sanya, jahad tabata riga da skirt na atampa da mayafi, sannan ita kuma hosana doguwar riga ce ta larabawa, baka sai ƴar guntuwar hijab fara, ba ƙaramin kyau su kayi ba,
Bayan sun shirya tsaf, ta haÉ—asu duka ta rungume ajikinta, gaba É—ayansu sukaji kuka yazo.musu nan suka shiga yinsa, sun jima kafin su fito,
daker aka samu goggon katsina tafito tayi musu sallama tasanya musu albarka idonta cike tab da hawaye, bayan sun kammala yi musu bankwana suka fito waje,
a jere motocin marshal Omar suke a harabar gidan, dakanshi ya buÉ—e musu motar da zasu zauna ciki suka shiga atare, sannan shima ya shiga motar dake bayan tasu ya zauna,
a natse ake driving ɗinsu har motocin suka fice daga gidan, suka miƙi hanya har suka fi ce daga welcome To katsina,
(* New destiny has started), 😥*💋💋
ABBAN SOJOJI💋💋💋
0 Comments