"; Abban Sojoji Chapter 15 Book 2 Hausa Novel

Abban Sojoji Chapter 15 Book 2 Hausa Novel

 

```The father Of Soldiers```

        

Story 

     &  

       Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)


Har haÉ—a baki suke yi wurin cewa "mahifinmu kuma ! A waya !?.

   Da Æ´ar dariya a fuskarta tace"Eh mana, ae kullum sai ya kira ni mungaisa,'  tayi maganar ayayin da ta kama hanyar zuwa bedroom É—inta don ta É—auko wayarta, 

  Hannu suka aza akai alamar sun shiga uku,  ita kanta saude tama rasa me zatayi abun ya É—aure mata kai, lamarin goggo sai addu'a tsufanta da rigima yazo mata, 

"Kada ku damu kunji kawai, ku kwantar da hankalin ku, in ta kawo muku wayar ku amsa ku gaisa dashi amatsayin mahaifinku, Uncle sufyan ya riga da yasan rigimar Goggonmu wayayye ne shi zai fahimce ku," 

  Saude ce tayi musu wannan bayanin, jiki amace suka amsa mata da cewa "Toh," 

 Sannan ta juya ta koma kitchen saboda tabar girki saman gas, 

Zuru su kayi suna jiran zuwan gaggon katsina da waya, babban tashin hankalinsu yarda zasuyi waya da mutumin da goggo ta Æ™aÆ™aba musu a matsayin mahaifinsu wanda basu ta6a gani ba kuma basu san kowanene shi ba," 

       suna nan zaune zuciyarsu nata bugawa sai ga goggo ta fito daga É—akinta, hannunta riÆ™e da waya sai faman zabga murmushi take yi,

Koda su ka ganta gabansu ne ya faÉ—i rass don su a tsorace suke, 

  MiÆ™a musu wayar tayi tare da cewa "Maza ga mahaifinku nan akan layi kuyi masa magana," 

  Kamar bazasu kar6a ba haka su kayi daker Jahad tasa hannu ta karbi wayar goggon tare da karawa a kunnanta tace ,"Assalamu alaikum," 

  daga can 6angaren taji wata natsattsiyar murya ta amsa mata da cewa "Wa'alaikum salam," 

  sai da jahad tayi jimmmm kafin ta daure ta cije tace "Abba Jahad ce É—iyarka, ina fata kana cikin koshin lpy," 

Abusufyan ya amsa mata da cewa "lpy lou Alhamdulillah My daughter, kin yi missing É—in abbanki kuwa,"? Yanda yayi maganar ba  Æ™aramin kashe ma jahad jiki yayi ba, sai kawai taji hawaye na Æ™okarin zubo mata, 

Murya na rawa tace "Nayi missing É—inka sosae abbana, ina kewarka," tayi maganar  ayayin da take dab da fashe wa da kuka, cikin sauri tace "Abbana ga hosana ku gaisa, itama tayi kewarka sosae," 

 "Okey bata wayar," ya umarce ta, 


Miƙawa hosana wayar tayi jikinta na kerma, hannu hosana tasanya ta karbi wayar tare da karawa a kunnata, duk goggo na tsaye tana kallonsu sai faman murmushi take yi, (ta haɗa Bomb)


  Tashi jahad tayi cikin sauri ta wuce bedroom É—in saude tana shesshekar kuka tana idasa shiga É—akin  ta faÉ—a saman gado tare da fashe wa da matsanancin kuka, bakomai bane ya karya mata zuciya ba face tunda suke arayuwa basu ta6a sanin daÉ—in soyayyar mahaifi ba ga Uban amma bai da amfani," 


Download>>> Jiddertul Khair Complete Document


  A can kuwa tun da hosana tasanya wayar a kunnanta tace "Abbana dagaske kaine mahaifin mu kamar yadda goggo ta faÉ—a," 

  On the other hand abusufyan yace "My daughter are u doubting abt ur father? nasan kinyi kewata ne shiyasanya kike kokwanto akaina," 

   aikuwa jin ya tabbatar mata da cewa shi mahaifinsu ne yasanya ta fashe masa da kuka tare da cewa "dama nasani kaine mahaifinmu, ba wancen mugun ba, sai da nace ma Oumma mu bamu kama dashi mummunane shi mai baÆ™ar zuciya amma taÆ™i yarda, ni nasani ba abban mu bane, babu uban da zaiyi wa Æ´a'Æ´ansa haka, kaine mahaifinmu,......"

Katseta yayi tare da cewa "Silent pls, sorry my daughter bana fahimtar zancen ki i was busy now, zan kira anjima,' 

  yana gama faÉ—an hakan ya kashe wayar saboda baisan inda zancen nata ya dosa ba, shi dai kawae ya amsa kira ne kamar yadda goggonsu ta sanar dashi cewa Æ´a,Æ´anshi sun zo, sarai yasan rigimarta shiyasa yabisu a hakan,

  Ganin ya katse kiran yasa hosana fashewa da kuka, wurgi tayi da wayar goggon saman kujerar sannan itama ta miÆ™e tana ci gaba kuka ta wuce É—akin saude, 

   Jikin goggo yayi sanyi, ita a tunaninta abusufyan bai kula da  yaransa shiyasa suke kuka, don haka taci alwashin zata sashi dole saiya zo nigeria ya É—auki Æ´a'Æ´ansa ya koma dasu can qasar da yake zaune, a ranta tana cewa "in banda shiririta irin ta abusufyan ka kama hanya ka tafi Æ™asar TurÆ™iya kabar yara cikin damuwa, gashi nan sai faman kuka suke yi, Allah ni da kai ne, saina sanar wa AMMI halin da ake ciki, 

 Ta idasa maganar tata tare da sa hannu ta É—auki wayarta ta wuce dakinta tana ci gaba da surfa bala'e akan rashin adalcin abusufyan, 


 ............................................SEHRISH.........................

tun da suka koma ciki take jin zuciyarta wasai, hankalinta kuma ya Æ™ara kwanciya yanzu, 

Gaba É—aya matasan gidan sun kammala dinner É—insu kowa ya koma bedroom É—insa, 

  Babu kowa ita kaÉ—ae ya rage ta kai wa Babban yayansu dinner É—insa, shine kaiwa bai sauko yaci ba, dama azmee tace sometimes kai masa ake a part É—insa, 

  Tsoranta kar yayi mata abunda yayi mata da safe, wato da yayi watsi da tray É—in hannunta, 

   A natse take tafiya zuciyarta na É—ar É—ar hai ta haye upstairs ta wuce part É—insa da sallama ta shiga babu kowa aciki, agyare yake tsaf haske ta ko'ina ga ni'ima acikin palor insa, 


  A hankali tasanya kafa tashiga ta Æ™arasa gaban table É—insa ta ajiye tray É—in ta tsaya riqe da Æ™ugu tana jiran fitowarsa bin ko'ina take da kallo tana Æ™ara jinjinawa haÉ—uwarsaa, .

bakomai ke fisgarta ba fa ce sanyayyan ƙamshin dake tashi tana burin wata rana ta samu damar da za ta ɗan miƙe ƙafa a saman 3 seater ɗinsa ta kwanta, 😌😒


Sauko Æ™afarsa yayi fara tass babu takalmi a kafar jikinsa na sanye da sleeping dress red color masu laushin gaske, jikinsu akwai zanene flowers masu kyau, riga da wando ne abunka ga handsome stylish man ga kira sun bi shape É—in jikinsa kai kace don shi akayi kayan, kyau kam ba'a magana ku kun sani ae, 

   tana cikin wannan kalle kallen idonta ya hango mata shi to fa nan take ta rasa duk wani karsashi na jikinta, bin shi kawai take da kallo, cike da wannan tafiyar tasa ta nigogin basawa ya karaso hannunsa É—aya na cikin aljihun wandonsa, halittar kyawunsa ta kara fitowa sosai daga saman rigar Æ™irjinsa a buÉ—e yake farar fatar sa ta bayyana muraran, 

   Sai kamshi jikinsa yake kamar wanda aka tsamo daga kogin turare,

Ga sumar nan tasha gyara sai salÆ™i take tana É—aukar ido, 

Zama yayi yana naÉ—e hannun rigarsa, 

Sai da rishi ta dai dai natsuwarta sannan tace "Barka da fitowa Babban yaya,"

"Yawwa," ya bata amsa a takaice, 

Har cikin ranta jin daÉ—in muryarsa take saboda yanayin yadda hausarshi ke fita irin ta wanda bai Æ™ware ba, 

Cikin girmamawa sehrish ta sake cewa "Me kake buƙata na zuba maka,'?

  ta tamabaya saboda kartayi ba dai-dai ba, 

"Abun da ya dace," ya bata amsa, 

Murmushi tasaki tana kallon face É—insi musamman gashin girarshi da eye lashes É—insa, 

Hannu tasa ta buɗe plate ɗinda ke ɗauke da friend meat (tsiran nama) yasha kayan ƙamsi yaji mai yaji komai,

 tura mishi tayi agabansa sannan ta É—auki bottle milk ta zuba mishi a glass cup ta ajiye masa, 

   bayan ta gama ta É—an ja da baya tana Æ™are masa kallo, yanayin yadda yake É—aukar tsiren yana turawa a bakinsa ba Æ™aramin kyau yayi mata, ji take ina ma da hali ta bashi abaki saboda ta sauÆ™aÆ™e mishi wahalar ,😒

  Wayar sa ce dake ajiye cikin bedroom É—insa  ta soma ringing da sautin gaske taken wakar nan ta  Imran khan (Satisfya) wadda yake cewa "am rider,provider, bring the heat girl i will bring the fire," 

   gyaran murya yayi tare da cewa "My phone," cikin sauri sehrish ta wuce bedroom É—insa asaman pillow ta samu wayar É—auka tayi jiki na rawa kamar ta riÆ™e bomb haka take ji, ta riÆ™e wayar manya ba, 

  Fitowa tayi da sauri taje ta miÆ™a masa, sai da ya fara cirar tissue ya goge hannunsa sannan ya sake tearing É—in wani acikin hannunsa sannan ya miÆ™a hannu ya karbi wayar  tare da picking call É—in ya kara a kunnansa,


Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!


Zuru sehrish tayi tana jira taji mai zai tattauna acikin wayar, sai dai kash cikin harshen spanish yake magana kalma É—aya ce sehrish ta tsinta, da taji yace "Mom," 

  Jinjina kai tayi aranta tace "Ina ji da mamansa yake waya, ashe mahaifiyarsu na nan, ko tana ina ne ita?

  ta, tambayi kanta ba amsa, 

babban burinta yanzu shine su haÉ—a ido dashi atlease yasan da zamanta sam bata tunanin hakan zai iya janyo mata matsala acikin gidan,

       A tunanin sehrish SGR bai ta6a kallota ba, tabbas hakane amma rana ta farko da tayi masa 6arin fruits a bedroom É—insa, ya hangeta ta cikin mirror ya ganta a matsayin namiji tsaye cikin fargaba a time É—in, duk da bai shaida kamannin fuskarba amma yasan cewa namiji ne mai kula dashi wato É—an aikinsu,'

Kammala wayar yayi tare da mayar da wayar ya ajiye gefensa, yaci gaba da cin dinner É—insa sehrish na saving É—inshi in ya kammala da wannan ta zuba mishi wancan haka suke abun nasu,

 Goya hannayenta tayi a Æ™irjinta tana kallon sumar kanshi ba Æ™aramin jan hankalinta Sgr yake yi ba, hakan yasa bata gajiya da tsayuwarda take yi na saving É—inshi tamkar mirror haka ya koma mata, tana cikin masa wannan kallon muryarsa ta ratsa ta da cewa "Kallon ya isa haka, ko saina shaÆ™e ne," 

Cikin sauri da jin kunya sehrish ta mayar da idonta ƙasa tana mai mamakin yarda akai Sgr yasan cewa tana kallonsaa murmushi tasaki saboda jin daɗin mgnarsa tabbas tana ji aranta cewa yana da sauƙin kai he's not arrogant kamar yaddda ta ɗauka,

...................... ..,,.....................................


A tsiyace ya shigo da motar layin gidan a dai dai gate É—in gidan ya dakatar da ita, ya shiga buga uban horn kamar zai tada motar gaba É—aya saboda karar da take yi,  

     "Kai!! uban waye ke mana horn haka,"? É—aya daga cikin sojojin dake gadin gidan ne ya tambaya da É—aga murya, akwai yasamu amsa dai dai dashi sai ji yayi ance "Ubanka ne kazo ka duba," 

       Abun ya basu mamaki aiko afusace sojojin nan suka tunkaro motar kamar wasu zakuna har haÉ—a hannu suke wurin buga glass É—in motar tare da cewa "Come out !! ," 

     "Ae basai kunbar umarnin na fito ba, É—an tasha ne ni dai dai daku," 

     Zuge glass É—in motar yayi tare da sa hannu ya cire Æ™umeman glass É—in dake manne a face É—insa yace "Akwai magana,"? 

Shiru su kayi dama ransu ya basu cewa shegen ne, ae duk duniya ba mai musu haka sai shi tantirin É—an duniya, 

  Bama cikin hayyacinsa yake ba ae mafi yawancin lokaci a buge yake yasha yasha har takai masa karo," 

   dogon tsoki ya buga tare da cewa "abani hanya na wuce kona bi takan mutun ba ruwana, kuma in na kashe mutun na kashe banza abanzance," 

   Ransu yayi mugun 6aci a dole suka matsa mishi ya shige babban gate É—in gidan da motarsa yana raira waÆ™a," 

  Parking É—in motarsa yayi sannan ya fito hannunsa riÆ™e da kwalbar giya, jikinsa na sanye da t-shirt baÆ™a sai wando crazy jeans É—innan ne, wani irin É—an iskan aski ne akansa na shaiÉ—anu jigunannun Æ´an duniya gefe da gefe an aske sumar kan, tsakiya kuma an mikar da wata tsaye ba ladabi, wuyansa na sanye da sarÆ™a yayin da kunnansa ke manna da earrings kai kace ba musulmi ba, saboda kwata kwata bai kama da musulmai ma, don kyau fa akwai kyau kana ganinsa ka ga bafullatani sak, duk da ba fari bane sosai amma yana da hasken fata mai kyau, yana da tsaga ta fulani agefen fuskarsa, 

  daker yaja Æ™afarsa izuwa cikin babban falon gidan babu kowa aciki wayam, É—aga murya yayi yadda kowa zaiji sa yace "NADAWO !!!! Hhhhhhhhh Woooo !!  Yaro ya dawo gidan Ubansa !!! Abba !! Gani fa nadawo !! É—anka HAROON ya iso dira ta kenan na Æ™aro sabon wulaÆ™anci buhu buhu hhhh, 


Download>>> Budurwar Mijina Complete Document


   Gaba É—aya hayaniyarsa ta cika musu kunne kamar zararre haka yadinga sambatu, 

   Ba arziÆ™i suka soma fitowa kowa jikinsa sanye da kayan bacci kanal yousouf ne yafara fito wa yana buga tsoki sai Khaleed da jabeer da irfan kowa ido cike da jin bacci ya katse musu baccinsu, atare twins suka sauko daga upstairs hannunsu cikin na juna sai hamma suke yi,,

   Abba ma tare da junaid suka fito sanye cikin phyjamas hannunsu cikin na juna, kowa sai faman buga tsoki yake yi a Æ™untace, tun da suka ga Commender haroon gabansu ya faÉ—i hankalinsu ya tashi ainin, sam babu mai farin ciki da zuwanshi duk da kasancewarshi É—an uwansu na jininsu amma munanan É—abi'unsa da halayyarsa tasa sun tsane shi sbd mugune na bugawa ajarida, 

Cike da takaici suke kallonsa kwashewa ya sake yi da dariya tare da cewa" Æ™ananin Æ´an iska sun bayyana ga kuma fararen balbelu," yayi maganar yana nuna su Twins da fawan da hannu É—aure fuska su kayi har time É—in ba wanda ya tanka masa binsa kawai suke da ido, 


  "Kutmelisiiii! Ni kuka maida shashasha ina magana kowa ya zubamin ido wato ga zautacce ko?baku farin ciki da zuwana ne, ae nayi tunanin ina zuwa zaku watso aguje kamar karnuka  ku rungumeni ku sunbace ni muuuaaah a baki na,' cike da futsara Haroon ke musu magana baya jin kunyar Abbansu,

Gaba É—aya duk wannan suratan da Haroon yake yi a kunnansa kaf ya gama fusata yagama hasala, aiko a harzuÆ™e ya Æ´unkura tamkar zaki yabi ta gefen Sehrish ya wuce ita kanta ta tsorata sosai ganin yadda Sgr ya fusata, 

   A wani irin slow sauri sauri yake tattakowa izuwa downstairs É—in, yana idasa sauko wa kai tsaye inda haroon yake tsaye riqe da beer a hannunsa ya tunkara, 

  Kanal yousouf ne kawai ya lura dashi wani shu'umin murmushi yasoma saki saboda yasan mai zai faru, 

   Haroon na cikin wannan sambatun baiyi wani aune ba yaji saukar wasu zafafan maruka ajere saman kuncinsa,

 

  Sai gashi Æ™asa baje saman tiles idonsa na facing sama, wato wasu irin black stars yagani a Æ™wayar idonsa masu wutsiya, kowa dake wurin bakinsa kumshe da dariya, 


  Sgr kuwa kara naÉ—e hannun rigarsa yake yi, 

   daker haroon ke kallonsa muryarsa na rawa yace "Ya Allah ka yafemun in zunubi nayi ka haÉ—ani da wannan Ifritun minal jinnin, wlh danasan cewa kana acikin gidan da ba abunda zai kawo ni, Abba mai yasa baka sanar dani cewa Babban yaya na cikin gidan nan ba...? Yayi tambaye agalabaice har lokacin bai samu ya miÆ™e ba yana daka kwancen yake sambatun nasa idonsa na kallon ceilling, 


   mayar da hannu Sgr yayi ya damÆ™i wuyan rigar haroon da hannu guda ya É—ago shi tare da Buga shi Æ™asa ya Æ™ife a susuce, shin wai ina kwalbar giyar dake hannun haroon ae tuni tayi gefe guda ta tarwatse, 

  Ganin Sgr na Æ™oÆ™arin sake kai hannu yakaiwa haroon wani naushin yasanya abban su cikin sauri ya riÆ™o hannusa yana cewa "Ya isa haka pls rabu dashi ae yaji jiki," 

   Jinjina kai Babban yayan yayi yana cije lips É—insa da ace abba yabarsa wannan naushin da yaso yakaiwa haroon da to tabbas sai yayi jinya a gadon asibiti, 

    É—agowa haroon yayi ido luhu luhu yana kallon babban yayan nasu murya na rawa yace "Yanzu babban yayan mu don rashin imani ka daddage ka dunkule wannan hannun naka Æ™irar samudawa da adawa bakaji komai ba ka jibge ni agaban Æ™anne na,"? yayi maganar akasalance yana kallonsa, 

  Wato bai daddara ba rae abace sgr yace "kai wai waye ya kawo wannan É—an iskan acikin gidan nan !?

  "Da Æ™afafuna nazo," haroon ya bashi amsa a raunane, mayar da idonsa yayi akan haroon yana huci in ya biyewa haroon to tabbas zai iya halaka shi a wurin nan, don shi bakinsa bai mutuwa ana bugunsa yana magana sai dae akashe shi,  


Dariya kawai junaid ke saki bama shi kadae ba hadasu irfan da sauransu in ka cire Kanal yusif da fuskarsa ke adaure shida babban yayansu, 

 duk wanda abun dake faruwa a kunnan sehrish tun da babban yayan nasu ya fito itama tabiyo bayansa, tana 6oye abayansa shi kansa baisan da mutun ba, sai dae ta leÆ™o ta saci kallon haroon dake baje yana sambatu ta takoma ta boye kanta, hakanan taji bai burgeta ba tunda taga fuskarsa taji bai kwanta mata arai ba, 

   junaid ne kawai ya lura da ita, amma ita bata ganshi ba, sai yi mata alama yake yi da hannunsa alamar ta matsa daga bayan babban yayan nasu, saboda gudun idan zai juyo kar yayi wurgi da ita, amma ita sam bata lura ba, 

"Dad pls kabarni na koyawa bastard ɗinnan hankali," ya faɗi yana kallonsa a ƙule

Haroon yace "hankali kuma na yaushe babban yayan mu ? ae tun ranar da ka fara aza tafin hannunka a kunci ne na zama cikakken mai hankali," 

   Æ™okari fa Rafayet yake na ya janye  hannunsa daga na abbansu yakai wa haroon bugu, amma abban ya hana hakan saboda tsoran karya naÆ™asa shi, 

Sam bazai  iya jure kallon haroon ba a fusace ya zame hannunsa daga na abbansu tunkan ya juya junaid yayi hanzarin riÆ™o hannun sehrish ya janye ta, ita kanta ta tsorata da ganin yadda sgr ya juyo tabbas da baÆ™aramin buguwa zatayi ba, cikin hanzari ya haye upstairs azazafe yake tattaka steps É—in benen ya wuce part É—insa, 

  "Kowa ya koma bedroom É—insa ya kwanta," kanal yusif ne ya basu umarni duk suka juya shima ya wuce nasa É—akin,

Ya rage daga Abbansu sai junaid sai sehrish dake gefe boye bayan junaid tunda ya janyota gabanta ke faÉ—uwa,

Kallonsu yake fuskarsa kamar zai fashe da kuka yace "Abba akan idonka yaran nan duk sun raina ni, ba wanda yayimun tarbar arziki shikenan ba komai ni daga nan zan koma inda na fito," 

  yayi maganar yana Æ™oÆ™arin tashi cikin sauri junaid ya Æ™arasa inda haroon É—in yake gaba É—aya yasa hannu ya rungumosa cikin sanyayyiyar muryarsa yace "Yaya haroon ni ina farinciki da zuwanka sosai, i missed u so much ka tambayi Abba kaji kullum saina ce mashi yaushe yaya haroon É—ina zai dawo, (Allah sarki junaid wato shi na musamman ne, kowa nasa ne baya gudun kowa, baya son ganin kowa cikin damuwa burinsa koda zai rasa nasa farin cikin indae hakan zai farantawa wani to tabbas zai rasa nashi,)

  hannu haroon yasa ya Æ™ara Æ™anÆ™ame Junaid tare da cewa "Dama nasani junaid kai kana sona sosai, kai kaÉ—ae ne ka damu dani, Allah sarki É—an uwa mai daÉ—i,"


Download>>> Macijine Complete Document

 

  "Nima ina farin ciki da zuwanka haroon, ka ta6a ganin inda uba ya guji É—ansa ? najima ina jiran ranar da zaka dawo saboda nayi kewarka sosae," acewar abbansu, 

Farin ciki ne ya lullu6e haroon cikin hanzari ya miÆ™e bayan sun rabu da junaid  ya rungume abbansu yana cewa "nasani Abba kaima kana farin ciki da zuwana," 

Juya junaid yayi ya kalle sehrish wadda take tsaye kamar gunki alama yayi mata na cewa itama ta gaishe da yayan nasu haroon,

Murya na rawa tace " Sannu da zuwa yaya haroon, nima ina farin ciki da zuwanka," 

  tun da muryar rishi ta ratsa kunnansa a wani irin yanayi ya É—ago da idonsa ya kalle ta, sai taji gabanta yayi wani irin mugun bugu har ta É—an firgita a bayyane, 

A wayance haroon ya saki murmushi tare da cewa "Wow junaid wanene wannan ko friend É—inka ne,"? Ya tambaya yana kallonta, 

  Junaid yace "a'a mai aikin mu ne tukur bai jima da fara aiki a gidan nan ba," 

Lumshe ido Haroon yayi yana kallonta duk tsigar jikinta ya tashi saboda kallon da haroon yake yi mata ba irin kallon da namiji keyi wa ɗan uwansa namiji bane, wani irin kallo ne dake nuna cewa akwai wani abu a ƙasa,

daker ya janye idonsa daga face É—in sehrish yana ci gaba da sakin wani shu'umin murmushi, 

   "My son ya kamata kaje ka huta a brdroom É—inka dare yayi ssae, gobe zamu tattauna mu Æ™ara gaisawa ko,'?

  abba ya tambaya yana kallonsa, haroon yace "hakane dad, but ina buÆ™atar abunda zan sawa ciki na, a sanya wannan mai aikin tukur yake da suna ko wama ya kawo mun abinci naci," ya kare maganar yana yatsina fuska,

Cikin sauri sehrish tace "shikenan bari naje na kawo maka," a tunaninta a nan zai ci saman dining,

Amma sai muryarsa ta katse ta da cewa "a bedroom  É—ina nake so akawomin junaid ka nuna masa É—akina pls," ya faÉ—i hakan tare da wuce wa yana cewa Abban nasu "Good nyt abbana," 

  Abban ya amsa masa da cewa "Sleep well my son,"

  ji tayi zuciyarta na bugawa, tunda ta haÉ—a ido da haroon taji tashin zuciya, wuce wa abbansu yayi shima bedroom É—insa yana barwa Junaid sakon ya same shi acan É—aki su kwanta," 

  Tsayawa su kayi suna kallon juna murmushi junaid ya sakar mata tare da cewa "Muje kitchen ko? ki haÉ—a wa yaya haroon abincinsa,' 

 itama murmushin tasakar mata tare da cewa "toh, amma babban yaya fa? inaso naje na idasa saving É—inshi abinci,

"Shikenan kije wurin babban yayan namu, ni bari naje kitchen na shirya masa abincin nakai masa," 

Wani daɗi ne ya rufe rishi dama batason zuwa wurin wancan baƙuwar fuskar da ta gani yau a gidan,

"nagode junaid," ta faÉ—i cikin sanyin murya, 

Junaid yace "Never mind ina yinki sosai," wuce wa su kayi ita takama hanyar upstairs shi kuma ya miƙi hanyar zuwa kitchen suna tafiya suna waiwayon juna,

Time É—in da ta shiga part É—in babban yayanmu samun shi, samu tayi babu shi a falon nasa alamar ya kammala cin abincin nasa kenan, 

 tunanin kwashe kayan abincin tayi amma sam tagaza samun natsuwa burinta atlease tasan wane hali yake ciki don ta lura da yadda ya fusata akan wancen baÆ™uwar fuskar da taji sun kira da haroon, hakan yasa ma taji bai kwanta mata a ranta ba, 

 tana cikin wannan tunanin tajiyo muryarsa yana faÉ—in "who's there," 

Cikin sauri tace "Tukur ne mai aiki," 

"Ok brings my phone, i left it there on seater,"  yana acikin bedroom É—insa yake magana,

Murmushi sehrish tasaki cike da rawar kai tasanya hannu a saman 3 seater É—in, ta dauki wayar tashi bin ta kawai take da kallo waya sai kacw wadda aka Æ™era da zallar diamond saboda tsantsar kyau, juya bayan wayar tayi tana kallon sunan dake a jiki karantawa tayi a fili (SGR) 

Jinjina kai tayi tare da cewa full meaning É—insa na nufin SURGEON GENERAL RAFAYET, kamar yadda aunty azmee na faÉ—a, 


Download>>> Yaro Ne Complete Document



   da sallama sehrish ta shiga room É—in nasa ae tana É—agowa wa'iya zubillah cikin sauri ta sunnar da kanta jiki na kerma, tsaye yake daga shi sai shorts ajikinsa babu riga wannan surar tashi mai rikitarwa ta bayyana muraran, sehrish taga abunda yafi Æ™arfinta dole ta kawar da ido, 

  Da alama daga toilet ya fito don ga danshin ruwa nan ajikinsa, sai faman lumshe blue eyes É—insa yake alamar bacci yake ji sosae, 

     Æ˜arasawa tayi zuciyarta na bubbugawa kamar zata fito waje saboda tsoransa,

  MiÆ™a masa tayi hannunta nata faman kerma tamkar wayar zata faÉ—i, har time É—in fa sgr baisan ya idonsa akan na sehrish ba, itama kuma saboda shegen tsoransa har yau bata bari idonta ya shiga cikin nashi ba, duk da bata da burin daya wuce ta haÉ—a ido da shi~~~

   A Æ™oÆ™arin ya sanya hannunsa ya kar6i wayar hannunsa ya gogi nata, wayyo zo gaka yadda sehrish Æ™anÆ™ame idonta ruff ta cije lips É—inta saboda shock É—in da taji,

Tamkar tayi hugging ɗin sgr harka take ji saboda wani irin ƙamshi dake fesowa daga jikinsa,

muryarsa ce ta shige ta da cewa "thanks," bayan ya karbi wayar ya furta hakan batare da ya sa idonsa ba akanta,

      Tsaye tayi tana kallonsa har ya wuce izuwa saman shimfiÉ—eÉ—en round bed É—insa mai É—auke da wata irin haÉ—aÉ—É—iyar mattress irin wadda kai tsaye mutun na hawa zata lomatse dashi ga wasu irin lumtsa lumbutsan matasssan kai a jere dayawa, idan muka zo kan Blanket É—insa kuwa wayyo just speechless wani irin lallausan bargone nama rasa yadda zan kwatantashi, jibgege ne mai gashi gashi ajikinsa irin wanda mutun na shiga cikinsa ko baiyi niyar yin bacci ba nan take zaiji sa,

Sehrish fa bata bar room É—in nasa ba kai kace tare zasu kwana ne, 

  Shikansa mamaki yake na ganin alamar cewa har yanzu fa house boy É—innan bai bar masa part É—insa ba, kawai zubawa sarautar Allah ido yayi yaga iya Æ™arshen abun, 

  A natse a hankali ya kwanta tare da miÆ™er da dogayen kafafunsa harya so ya wuce gadon ma don Allah yayi sa da tsayi ga kuma Æ™ira abunsa duk shi kaÉ—ai,

 Zira ziran yatsun hannunsa yasanya tare da janyo blanket É—insa ya rufe har iya Æ™irjinsa, sannan ya É—an lumshe idonsa yana sauke ajiyar zuciya,

  sam tagaza janye idonta akanshi komai nasa burgeta yakeyi yana yin komai a natse ba hayaniya, 

Har bacci ya É—auke sa sehrish bata fita ba leÆ™en beautiful face É—insa take,  

  matsawa tayi a hankali dab da bed É—in nasa sannan ta É—an jinkirta ta shiga yi masa addu'a daga tsayen da take, addu'o'i sosae sehrish tayi wa Sgr batare da sanin shi ba don yayi nisa a cikin baccin nasa,

 Bayan ta kammala ta juya ta fice tana mai jin sanyi aranta har cikin ranta Sgr ya kwanta mata sosai, 

Cike da wannan shauƙin sehrish ta wuce nata room ɗin ta haye saman gadonta fuskar nan da murmushi, abu biyu take tunawa haɗuwarsu ta yau da junaid sai kuma Babban yayanmu, duk in ta rufe idonta shi kawai take gani sai juyi take cikin bargo cikin nishaɗi,

(Allah sarki na tausayawa sehrish sosae domin ta faÉ—a tarkon so, son ma wanda ba son maso wani ba wannan son ya zarce hakan domin ta faÉ—a tarkon son wanda sam bai ra'ayin mace arayuwarshi bai da burin yin aure har abada) 

________________________________________________hafsat Bature

A hankali motocinsa suka shiga cikin gidan yana zaune a back seat a hakimce ana driving É—insa, 

Bayan sunyi parking É—in motocin cikin sauri major É—in nan ya fito ya buÉ—e masa mota, 

 Fitowa marshal Omar yayi yana sauke ajiyar zuciya bakomai idonsa ke marmarin gani ba face wannan Zararriyar yarinyar da ta faÉ—a masa a chest É—insa da ita ya yini a zuciyar shi, 

  Ba shi kaÉ—ae bane tare da Babban likita suka dawo gidan, saboda dama nan ne makwancinsa, 


Download>>> Bakar Inuwa Complete Document


   Bayan sun shiga cikin main palor É—in agajiye babban likita ya wuce side É—insa, yayin da Marshal Omar ya samu wuri saman 2 seater, 

Shigowa major É—in nan yayi hannunsa É—auke da laptop É—insa ya miÆ™a masa, 

Kar6a Omar yayi tare da furta "thanks," sannan major É—in ya sara masa kafin ya fice,

Tsit bakowa sai shikadae a falon, aza laptop É—in yyi saman table  É—in dake a gabansa sannan ya zaro wayarsa daga trouser pocket É—insa, 

Zubawa wayar ido yayi yana tunanin wa zai kira ma domin a kira msa yaran yana son ganinsu kafin ya kwanta, bai son kiran goggon katsina don yasan halinta da rigima, gashi bai da numbar saude 

Zama.yayi shiru yana tunanin mafita, kamar daga sama sai ga jahad  ta fito cikin sanÉ—a ashe batayi bacci ba komai ya fito da ita Oho,

"Ke zo nan," 

Daram !! Taji gabanta ya faÉ—i rass jin muryar mutumin nan tsaya wa tayi a hankali tana kallonsa, 

Kafin ta tunkaresa zuciyarta na É—ar É—ar ta samu wuri Æ™asa tazauna tare da lankwashe Æ™afa ta gashe shi "Ina wuni," 

Bai amsa mata wannan ba sai ce mata yayi "where's your sister"? 

Jahad tace "Bacci take yi," 

"Je ki tasarmun ita, ina son ganinta,"

Mamaki ne ya kama jahad alamu sun nuna cewa marshal Omar fa yana iya banbance su tunda gashi ya nemi ta kira masa yar uwarta wato wadda ta faÉ—a masa ajikinsa, 

Kallo guda yayiwa jahad ya gane cewa ba ita bace wadda ta faɗa masa a ƙirjinsa ba, kaji masu aiki da kwakwalwa,

  farat É—aya ya karanci wani abu a tsakaninsu daga É—azu a asibiti zuwa yanzu, 

  tashi jahad tayi cikin sauri ta shiga É—akin kamar yadda tabar hosana haka ta same ta kwance a tsakiyar gadon ta lumbutse abunta, baki wangame sai sharar bacci take.tana hura hanci kamar SA, 

É—an bubbugata Jahad tayi tare da cewa "Hosana !! Hosana ki tashi," 

Tsoki taja tare da juya mata baya "Leave me alone," 

a Æ™ule jahad tace "wai baxaki tashi ba," 

"Eh baxan tashi ba, in kinji haushi ki É—auke ni mana," 

murmushi jahad tayi tare da cewa " to shikenan bari naje na ce masa kince baki zuwa," 

  jin abunda jahad tace yasa ta yin wani irin juyi ta Æ´unÆ™ura cike da zumuÉ—i tace "Wa,? 

ƴar dariya Jahad tayi tare da cewa"mutuminki mai ƙarfi," 💪

   Wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskar hosana, tasowa tayi daga saman gadon tana gaggyara rigar jikinta, hannu tasa ta É—auki mayafinta dake anan saman gadon ta yafa, 

Sannan suka fito atare ita da jahad É—in, Æ™arasawa su kayi gabansa riÆ™e da hannun junansu, 

É—agowa Omar yayi ya kallesu atare ya sauke idonsa kan Hosana wadda ke ta faman zabga mishi murmushi kamar gonar auduga,

"Have a seat," ya umarce su

Zama su kayi saman 2 seater É—in dake facing É—inshi, 

"What's Ur names,'? Ya tambaya yana ci gaba da danna laptop É—insa,

Cike da zumuÉ—i hosana tace "Ni sunana Hosana ita kuma sunan ta Jahad," 

Jinjina kai Omar yayi kafin ya kuma cewa "Wacece mai ta6in hankali acikin ku,"? Ya tambaya tamkar bai gane ta ba,

Cikin sauri hosana tace "Ni ce,' 

Murmushi kawai jahad ke yi shiriritar hosana nabata headache,

"Au kece kenan,? Ya tambaya yana É—an kallonta, 

Hosana tace "Eh nice bani da hankali but not always ynx ina cikin hankali na, 

É—an ta6e lips É—insa yayi kafin ya kuma cewa "Ina iyayen ku suke,"? 

  Shiru sukayi saboda sun rasa amsar da zasu bashi sai can hosana tace "Bamu da kowa, bamu son kowa ba, mu kawai muke rayuwarmu....' 

tunkan taƙarasa ya dakatar da ita tayi shiru , ci gaba da danna laptop ɗin dake gabansa yayi kusan 15 mins bai sake cewa komai ba sai dai ya ɗan ɗago da idonsa ya kalle su ya mayar,

"A matsayin me zaku É—auke "?

ya tambaya yana kallonsu har haÉ—a baki sukeyi wurin cewa "Yayanmu,' 

Jinjina kansa yayi tare da cewa "Good, as frm now na zama yayanku, a shirye nake dana ɗauki dukkan wata ɗawainiya taku daga yanzu kun dawo ƙarƙashin kulawa ta, komai kke so just feel free ku sanar mun ko wani abu na damunku haka, sa'annan ku shirya tafiya gobe domin ba'a nan zaku zauna ba, zan mayar daku kaduna state gidan ƴaƴana, zaku samu kulawa sosae acan,

   Har haÉ—a baki suke yi wurin yi masa godiya, 

"No bana son wannan, bana son ana min gdy, zaku iya tafiya gobe ku tashi da shirin tafiya, 


Download>>> Yar Harka Complete Document


MiÆ™ewa su kayi atare har sun É—anyi nisa sai kuma suka juyo suna kallon shi atare suka haÉ—a baki wurin cewa "Sai Allah ya kaimu yaya Omar," 

Ba Æ™aramin daÉ—in sunan yaji ba, jinjina musu kai kawai yayi sannan suka shige, shima tashi yayi ya wuce can cikin part É—in big doctor domin dama acan suke kwana in sun zo," 

"Hosana ya kika ji muryar mutumin nan na É—azu wanda goggon nan ta bamu mu gaisa dashi a matsayin mahaifin mu?

Jahad ce tayi wa hosana wannan tambayar ayayin da suke kwance su biyu saman gadon suna fuskantar junansu,

"A time É—in naji shine tamkar mahaifina Jahad banso ya kashe mun waya ba kuma yace zai kira da anjima amma bai kira ba," 

Ajiyar zuciya jahad tasaki kafin tace "Nima haka Hosana, tun da naji voice É—inshi naji zuciyata ta karye, shiyasanya na miÆ™a miki wayar sbd kukan da yazo mun," 

Hosana tace "dama ace shine mahaifinmu ko?

  jahad tace "how that can be possible, we already ave our own father hosana, so stop expecting that pls,"

Shiru hosana tayi suka zuba ma juna ido na wani lokaci kafin Jahad tace "Allah Sarki Sehrish nayi kewarta sosae kullum tunani ya rayuwarta take, yaushe zamu sake sanyata a idonmu duk in na tuna hakan sai naji tsananin Æ™unci da baÆ™in ciki araina, sehrish tasha wahala akan mu, tayi mana irin sadaukarwar da uwa ke yiwa Æ´a'Æ´anta, duk da kasancewar ko a wurin haihuwarmu Oumma ta faÉ—amin cewa sai da muka fara zuwa duniya da minti 30 sannan sehrish ta fito Allah sarki mai kyakkyawar zuciya insha Allah rayuwarki zatayi kyau Sehrish no matter what the situation is I wll neva stop praying 4 u, 

  ta daka da maganar a yayin da hawaye ke zubo mata daga eyes É—inta izuwa saman pillow É—in da take kwance,

  Jikin hosana ne yayi mugun sanyi itama murya akarye tace "duk nice Sila jahad da ace ban jefa wayar nan ba, da yanzu muna nan muna waya da ita har ma yaya Omar yakaimu wurinta........'

Kuka ne yaci Æ™arfinta har ta kasa Æ™arasa maganar da take yi, 

"Oumma ta faÉ—a min cewa mu ba Æ´an uku bane ta haifa, amma Abba ya kwashe sauran ya siyar dasu saboda shegen son kuÉ—insa, narasa wani irin uba ne shi ya azabtar da rayuwar mahaifiyarmu da kuma rayuwarmu Allah ya isa bazamu ta6a yafe mishi ba har abada..........

cikin kuka take magana itama hosanar kukan take yi domin komai ya faru arayuwarsu in suka tuna sai zuciyarsu ta karaya, mummunan Labari mara daÉ—in Ji 

Matsawa su kayi jikin juna suka rungume junansu suna ta faman shesshekar kuka Allah sarki kowa da irin tasa kaddarar, 😥

___________________________________________Hafsat Bature Moh'd


"Junaid menene haka wai"? Abbansu ne ke yi masa magana da bacci a idonsa, junaid dake saman chair É—in dake gaban mirror sai faman zabga murmushi yake ya juyo ya kalli abban nasu dake kwance saman gadonsu yace "Abba u will not understand it, Abba kasan yadda so ke shiga ? Yayi tambayar yana kallon Abban nasu,

Cike da takaici yace "Junaid taso kazo ka kwanta kayi bacci tunkan  raina ya 6aci,' 

"Hmmmm dad  kenan ka ta6a ganin inda Romeo yayi bacci ayayin da yake tunanin Juliet É—insa," 

shiru Abban yayi yana kallon ikon Allah lamarin junaid ya fara bashi tsoro, shi burin shi ya taso su kwanta amma  junaid ya Æ™iya, gashi in baiyi bacci da wuri ba daker ake tashin shi bacci wurin sallar asuba, 

Hannu Abban yasa ya daki katifar gadon da ƙarfi yace" Zaka taso ko bazaka taso ba"

Fari junaid yayi wa Abban nasu da ido, irin farin da mata keyi na ido yace" Daddy kaima kayi tunanin mommy mana, Nima nayi tunanin juliet É—ita,


Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!


 *BossLady* 💋 in kinaso ki saka mun kawai kimun share na novel É—ina 🪩🪩🪩 sannan In zakuyimun comment pls ba thanks nakeso naji mutun yace mun ba, kawai kimun comment da abunda ya burgeki ko wanda ya baki haushi, komai dae

Post a Comment

0 Comments

Ads