Gamo Complete Novel Document

A sukwane ya fito daga É“angaren da yake mallakin sa agidan. Kallo É—aya zaka masa ka tabbatar wannan É—an kwalisa ne, Yana sanye da riga fara Æ™al shirt Æ™irar kampanin Mk, da wandon jeans blue shi É—inma kamfanin Mk ne, agogon hannun sa Rolex ne wannan kuÉ—in sa zekai kimanin dalar amurika dubu goma! Akwai zoben a hannun sa  wanda ya Æ™arawa faratan nasa kyau. Takalmin Æ™afar sa baÆ™aÆ™e ne normal shoe Æ™irar kamfanin Mk. Ƙamshin turaren sa yana mamayar duk duniyar daya nufa sabida tasirin sa, Turaren Tomford the king   ne ajikin sa, haÉ—e da wani Arabian king oud! Fuskar sa ba fara bace sam sedai bazamu kirashi baÆ™i ba, kyakyawan daidai kyawawan Æ´aÆ´an hausawa, fuskar sa tana É—auke da tsawo da É—an faÉ—i kana kuma akwai zagayyayen saje wanda yake haÉ—e  da kwantacciyar sumar kansa, yayi zagaye zuwa gemun sa. Yanada wushirya bakinsa a zagaye yake da laɓɓa masu É—an tudu sedai É“a cen cen ba. Yanada dogon hanci samÉ“al tare manya manyan dara daran idanuwa dasukeda yalwar fari, baÆ™in zagayen idonsa daga ciki baÆ™i ne amma a gefen sa yaÆ´i kalar bulu. Yanada tsananin cikar halitta zamu iya cewa Æ™irar sa tafi kamada Æ™irar samudawa madaidai ta. Kana kallon sa zakaga Æ™arfafan mutum dankuwa nonuwan sa tas sun cike Æ™irjin sa, ga 6 parks ruÉ—um ruÉ—um a cikin sa, Æ™asan sa ya tsuke amma kafaÉ—unsa da faÉ—i cikakken mutum me kamala. 

  Da É—an sauri ya isa cikin falo na É—aya inda ya tsallake wannan falon yayi kutse zuwa falo na biyu har zuwa matakin na uku inda ya tarar ana yiwa mahaifiyar sa Makeup zataje taron Æ™arawa juna sani da aka gayyace ta. Zubewa yayi ya gayar da ita cikin girmama wa, da fara'arta ta amsa  masa sannan tace,


"Hakeem sai ina kuma?" 

Murmushi yayi sannan ya ce


"Maganar tafiyar damuka yi ne lagos Ummi, flight namu ze tashi by 11 this morning" Ɗan ɓata fuska ta yi,


"Amma ba nace ka dena zancen tafiyar nan ba sai next week Hakeem?" Sosa kan sa yayi cikin jin nauyin abinda zai faÉ—a kafin yace,


"Ummi Nihal, fa tafiya zatayi yau itama, dan Allah ki barni naje, tafiyar ta aiki ce, yanada muhimmanci sosai kuma" Nisawa tayi ta zaro  wayar ta cikin damuwa, 'har sai yaushe Nihal da Hakeem zasu basu haÉ—in kai a harkar nan?' Ta ayyana a ranta, tana me kiran wayar Babbar aminiyar ta wato Hajiya Baraka mai gwal. Da Sallama ta É—aga call É—in ta tana fara'a suka gaisa sannan ta ce, 


"Hakeem yace Nihal bata gari?" Murmushi ta yi sannan ta ce,


"Nihal gatanan a kusa dani, tabbas tafiya takeso tayi  amma Daddyn ta ya hana ta banda kuka ba abinda take" Sauke Numfashi tayi kafin ta ce,


"Hakeem ma gashinan ya kafe akan lallai seyaje Lagos, tafiyar aiki ce, ya zamuyi kenan?


"Your Excelency ki barshi ya tafi, koda kin hanashi a yanayin yanda Nihal take bazata bamu haÉ—in kai ba, inyaso idan ya dawo semu zauna" Godiya tayi mata tare da sallama sannan ta ajiye wayar taci gaba da baiwa me makeup.haÉ—in kai batare data kuma waiwayar Hakeem ba, shikuwa yakai 40mns har aka kammala makeup bata bashi izinin tafiya ba, ta miÆ™e zata fice yabi bayan ta har wurin mota, seda aka buÉ—e mata ta zauna sannan ta rage glass ta kalle shi, duk yayi kalar tausayi 


"Hakeem wai menene? Tamkar zeyi ƙwalla ya ce,


"Addu'a Ummi tafiya fa zanyi" kawar da kanta tayi gefe,


"Inada taro Allah ya kiyaye" Ta zuge glass sama ta bada izinin tafiya take convoy ya tashi. Sumar kansa ya shafa cike da damuwa, 'Ummi duk in zeyi tafiya takan dafa kanshi ta masa addu'a mesa zata masa haka yanzu kuma?' Agogon hannun sa ya kalla sannan a ƙagauce yabar wurin zuwa wurin motocin dasuka jeru sama da goma suna jiran sa, faɗawa yayi yana me addu'ar neman kariya ta barin gida.

WRITTEN BY:     BILLY GALADANCI

NOVEL NAME:   GAMO COMPLETE

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         364KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:      18- MAY -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            ₦300

Proceed To Download Gamo Hausa Novel Document.



Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!



KARANTA LITTAFIN: "TUBALI BOOK 1 CHAPTER 1"



KARANTA LITTAFIN: "TUBALI BOOK 1 CHAPTER 2"




Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More



Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com


Post a Comment

0 Comments

Ads