Fitacciyar Jarumar Kannywood, Aisha Najamu Tayi Bikin Cikarta Shekaru 28 A Duniya (HOTO)


 Jarumar Kannywood, Aisha Najamu wacce aka fi sani da suna (Aisha Izzar so) ta saka wasu kayatattun hotuna a shafinta na instagram yayin da take murnar cika shekaru 28 da haihuwa.  Jarumar Kannywood, Aisha Najamu na daya daga cikin hazikan jarumar Kannywood a cikin shirin da yafi kowanne shiri farin jini mai suna Izzar so.


 Aisha Najamu kuma da wasu Furodusoshi ke nema a halin yanzu, tauraruwarta tana kan ganiyar haskawa a masana'antar fina-finan ta kannywood.


 Kalli Wasu Hotunan Jarumar a kasa.


 


 

An haifi Aisha Najamu a ranar 7 ga Maris, 1995, iyayenta ne suka haife ta kuma suka rene ta a jihar Jigawa.  Aisha Najamu ta kammala makarantar firamare da sakandare a mahaifarta jihar Jigawa.  Bayan kammala karatunta na Sakandare aka daura auren Aisha Najamu, Inda Allah Ya yi wa auren albarka ta haifi 'ya'ya maza biyu kyawawa. Hotunan bikin Ζ™arin shekara na Aisha Najamu sun dauki hankulan mutane a shafukan sada zumunta musamman masoyanta na instagram.

Post a Comment

0 Comments

Ads