Amfanin Agwaluma a jikin dan Adam

 


Wani sabon binciken masu kimiyya ya nuna cewa za a iya amfani da ganyayyaki da itacen Agwaluma wajen magance zazzabin Malaria mai naci ko wanda bai jin magani.


Binciken wanda aka wallafa a kundin BMC Complementary and Alternative Medicine ya bayyana cewa wannan magani ka iya zama sabuwar karbabbiyar hanyar magance zazzabin duba da rashin nasarar da ake samu da sauran nau’ikan magunguna.


Masu binciken wadanda ‘yan Nijeriya ne sun gwada ingancin maganin a akan beraye da ke dauke da cutar, inda aka samu nasarar magance ta daga jikin su.


Masanan sun ce a nan gaba akwai yiwuwar za a koma amfani da saiwar Agwaluma da ganyayyakin ta wajen hada magungunan Malaria.


Izuwa yanzu, magungunan malaria da aka sani na kara rage karfi a yayin da suke daina aiki akan kwayoyin cutar nau’ika daban daban, wanda ba karamin koma baya bane ga yunkurin kakkabe cutar a fadin duniya.


Masu binciken sun ce wannan ne ya sa dole ne a fito da wasu hanyoyi na daban na magance cutar a cikin gaggawa, inda kuma amfani da Agwaluma na daya daga cikin irin wadannan hanyoyi.

Post a Comment

0 Comments

Ads