Akwai sabon shagali tafe: Jarumar Kannywood, Teema Yola za ta shiga daga ciki


Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa wacce tauraronta ke kan haskawa, Fatima Isa da akafi sani da Teema Yola na shirin shiga daga ciki.


A cikin yan watannin nan ana ta shan shagalin bukukuwa a masana’antar ta kannywood, inda zuwa yanzu aka daura auren akalla jarumai hudu da furodusa daya.


An fara ne da auren jarumai mata biyu a karshen watan Fabrairu wato Hafsat Idris Barauniya da Aisha Aliyu tsamiya, sai kuma na jaruma Hassana Moh’d wacce ta auri babban furodusan masana’antar, Abubakar Bashir Maishadda a ranar 13 ga watan Maris.


A yanzu kuma mun samu labarin shirye-shiryen auren Jaruma Teema Yola wanda abokiyar sana’arta, Umma Shehu ta sanar a shafinta na Instagram.


Koda dai Umma shehu bata bayyana ranar da za a daura auren Teema ba, ta tabbatar da cewar ita ce ta gaba a kan layi. Ta kuma wallafa bidiyon jarumar tare da wanda ke shirin zama angon nata.


Umma ta rubuta a shafinta:

“Ma’auratanmu nan gaba Insha Allah.” 

Post a Comment

0 Comments

Ads