Jarumar Shirin Labarina Ta Auri Tsohon Dan Wasan Najeriya


A yau ne muka samu wani labarin cewar a jiya Juma'a, 26 ga watan Nuwamba, 2021, ne aka daura auren fitacciyar jarumar nan ta cikin shirin Labarina mai dogon zango, wato Maryam Wazeer, wacce ta ke fitowa a matsayin Laila. 

Ita dai Maryam Wazeeri ta angwance da ƙwararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya wato super Eagles, Tijjani Babangida.

Also Read: Shin ko kunsan dalilin yin kidnapping din Sumayya a cikin shirin Labarina kuwa?


Daman tunda aka dawo daga wannan Season din ba a ga fuskar jarumar ko sau ɗaya ba, haka yasa wasu daga cikin mutane suka fara raɗe-raɗin cewar iyayenta ne suka hanata.Daga Ƙarshe muna addu'ar Allah Ya basu zaman lafiya ya kawo zuri'a ɗayyiba, yan baya ma Allah ya kawo masu mazaje na gari, Amin.

Post a Comment

0 Comments

Ads