Maganin Kaikayin Jiki Da Mara Ga Maza Da Mata

 


A mafi yawan lokuta idan muka yi wanka kaikayi kan damun jikin, hakan kansa mu rasa inda za mu saka kanmu, ko kuma ƙaiƙayin mara wanda mafi yawan wannan matsalar ta fi shafar mata, to yau insha Allahu zamu kawo maku yadda za ku magance wannan matsalar da ikon Allah sai dai a sani cewa shi magani sababi ne na waraka.

Ga mahaÉ—an maganin kamar haka don haka sai a natsu a karanta:

  1. Na farko a samu ruwa kofin shayi Uku
  2. A samu citta danya ko kuma wadda ta bushe
  3. A samu garin kanunfari karamin cokali
  4. A samu tafarnuwa curi É—aya ma'ana kwallo É—aya a daka ta.
  5. Sannan abu na karshe shi ne a samu garin kurkur shima cokali É—aya.

YADDA ZA A HADA MAGANIN

Wannan ruwan kofi Uku za a É—ora shi a wuta, sai a samu citta kamar guda biyar da tafarnuwa kwallo É—aya, amman ya zama cewar cittar da tafarnuwar an daka su, sannan sai a dauko garin kanunfari da kurkur a haÉ—e su duka a tafasa. Bayan sun tafasa sai a tace. A raba ruwan gida Uku asha da safe bayan anci abinci sannan asha da rana sannan sai da daddare.

AMFANIN WANNAN HAÆŠIN

Kafin mu fara faÉ—ar amfanin sa bari mu yi wani É—an bayani akan haÉ—in, shi dai wannan haÉ—in ana son ka samu kamar wata Biyu kana yi, 

  • Yana maganin sanyi mai sa tattare fatar jiki kuma ta yi baÆ™i.
  • Maganin sanyi mai sa kaiÆ™ayin matse-matsi.
  • Maganin sanyi mai sa yawan fitsari.
  • Maganin sanyi mai sa tsattsagewar matse-matsi.
  • Maganin sanyi mai sa Æ™aiÆ™ayin ido.

DOKA

Kada ka sha har sai ka ci abinci, sannan kowa zai iya sha amman banda yaron da bai kai shekara Uku ba.


Allah Ya bada sa a ya biya mana buƙata.

Post a Comment

0 Comments

Ads