Dalilin da yasa na ki auren Adam Zango - Jarumar Kannywood, Ummi Rahab Saleh

 Dalilin da yasa na ki auren Adam Zango - Jarumar Kannywood, Ummi Rahab SalehUmmi Rahab Saleh dai fitacciyar jarumar Kannywood wacce yanzu haka tana cikin wani babban rikici tare da uban gidan ta, Adam A. Zango, a karon farko ta bayyana cewa Zango ya ba ta shawara inda ta ki yarda kuma shi ya sa ya turo mata kaya daga gidan sa, ma'ana ya koreta daga gidan sa

 "Har yanzu ina girmama shi saboda lokacin da na zo Najeriya daga Saudi Arabia, inda aka haife ni, ya karbe ni hannu bibbiyu, ya taimaka min har na kammala karatuna kuma ya samar min aiki a Kannywood, kuma a kan haka, zanci gaba da yi masa godiya bisa kulawar da ya bani.

"Amma lokacin da ya gaya min cewa yana so ya aure ni, na ƙi, saboda ga mutumin da ya yi aure sau 6, tare da yara 6 daga mata daban-daban. Wasu daga cikin tsoffin matansa sun kasance daga masana'antar ta Kannywood su ke, don haka ni ai wawiya ba ce da zan aure shi, ina da wasu samari a rayuwata da nake so.


Also Read:

Maganar Gaskiya Akan Auren Hadiza Gabon Da Isah Ali Pantami


 Amma saboda tsananin kishi ya yanke shawarar ya fitar da ni daga gidansa, ya cire ni daga fim dinsa mai suna “Farin Wata Shakallo”, amma ba ni da nadama. Ina da rayuwata da zan rayu, yanzu na girma kuma zan iya rayuwa da kaina. Ku ba ni 'yan shekaru masu zuwa nima ina da tabbacin zan shahara, zan zama tauraruwa a cikin masana'antu'ar ta Kannywood tunda ba mutum ba ne ke bada daukaka Allah ne, don haka ina da yaƙinin nima Allah zai daukaka ni.

Shin kun san lokacin da na sami matsala da Zango, mutanen da ban taɓa haɗuwa da su ba sun zo wurina kuma a shirye suke su kare ni daga kowane fanni. Gaskiya, ina godiya sosai gare su da abokan aikina a masana'antar.

Post a Comment

0 Comments

Ads