Yadda za a magance tabo da kurajen fuska insha Allahu


Assalamu alaikum jama'a barkanku da wannan lokaci ayau insha Allahu zan sanar da ku hanyoyin da za a magance tabo da kuma kurajen fuska.

Mafiya yawan wadanda wannan matsalar ta fi shafa su ne matasa, maza da mata.

Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska amman sai tabo ya ƙi ɓacewa.

Hakika rashin ɓacewar tabo na ɓata kwalliya. Sau da yawa 'yan mata basa son shiga cikin taron mutane saboda taɓon da ke fuskarsu.

Masu wannan matsalar kan gwada mayukan kanti, domin dai rabuwa da wannan matsala ta tabon fuska, wasu kan samu nasara ya ɓace amman wasu kuwa baya ɓacewa.

Ayau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a sani cewa ɗaya za a zaɓa daga cikin hanyoyin da za mu yi bayani, kada a kuskura a haɗa su. Domin yin hakan zai ƙara lahanta fuska ne.

Hanya ta farko a samu gayen dogonyaro, sai a haɗa shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan ɗumi.

Hanya ta Biyu za a iya shafa markaɗaɗɗen dankalin turawa akan tabo. Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya hana su sake fitowa gabaɗaya.

Hanya ta Uku ita ce, a daka tafarnuwa sai a shafa akan tabo. Duk da tana da wari, amman tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.

Allah Ya sa a dace.Post a Comment

0 Comments

Ads